Rundunar ‘yansanda a Jihar Gombe ta kama Kansila mai wakiltar Kumo ta Gabas a Karamar Hukumar Akko da ke jihar Abdullahi Panda da wasu mutum biyu bisa zargin sata da sayar da taransfoma na al’ummar Majidadi.
Da take gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai bayan an kama su, kwamishiniyar ‘yansandan Jihar Gombe, Hayatu Usman, ta ce an kama wadanda ake zargin ne bayan da aka samu labarin faruwar lamarin.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta
- Xi Ya Gabatar Da Jawabin Cika Shekaru 70 Na Ka’idoji 5 Na Zaman Tare Cikin Lumana Tsakanin Kasa Da Kasa
Usman ta ce an sayar da taransfomar ce ga wani mai suna Bello Ardo Kumo kan Naira miliyan 1.5, inda ta ce ‘yansanda sun kwato na’urar kuma suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin bayan an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Hakimin Kauye ne Muhammad Majidadi ya bayyana cewa taransifomar ta shafe shekaru 10 ba ta aiki kuma a lalace take sannan an sace wasu sassanta.
Ya ce al’ummar yankin sun yanke shawarar sayar da taransifomar ce domin gina makarantar Islamiyya da kuma asibiti a kauyen.
Majidadi ta yi ikirarin cewa shi ne ya sanar da kansilan yadda za a yi, amma Panda ya musanta cewa yana da hannu a sayar da taransfomar, ya kuma bukaci a kai maganar kotu.
Bugu da kari, Hukumar Tsaro ta NSCDC, a Gombe, ta gurfanar da wani manomi a kotu bisa daure hannun Adamu dan dan uwansa da ya zarga da laifin sace wayar dansa lamarin da da ya kai ga hannun ya lalace har aka yanke.
Malam Yahaya Buba, mai shekaru 42 da ake tuhuma wanda ya daure hannun dan uwansa Mohammed Adamu mai shekaru 21, ya yi alkawarin bayar da tallafi mara iyaka ga wanda aka yanke masa hannu.
An ruwaito cewa hannayen Adamu sun yi rauni, bayan da aka daure na tsawon sa’o’i, lamarin da ya hana zagayawar jini daga sauran sassan jikinsa zuwa hannayen, wanda hakan ya jawo illa gare shi.
Tun da farko, Buba, wanda kawun Adamu ne, ya zargi dan uwansa, Adamu, da satar wayar dansa.
Buba, wanda manomi ne kuma mai wayar da kan jama’a, ya dora laifin afkuwar lamarin kan aiki ne na shaidan, inda ya ce dama kuma Adamu ya taba yin sata.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa, “Ni manomi ne daga Sambo Daje a Kashere, Masarautar Pindiga, Karamar Hukumar Akko. Na shuka masara da wake, wanda nake nomawa, ina da ‘ya’ya 10, amma biyu sun mutu a halin yanzu ina da ‘ya’ya takwas da suka rage da mata daya.
“Shi (Adamu) ya kasance yana shiga gidajen mutane don yin fashi, yana satar kayayyaki kamar awaki, shanu, da amfanin gona.
“A duk lokacin da ya saci amfanin gona misali, in buhu daya ya sata sai ya kona sauran amfanin, sanna a duk lokacin da aka kama shi suka gaya min na kan roki gafararsu su bar shi ni a yi min horo,” in ji Buba
Da yake tsokaci a kan dalilin da ya sa ya zabi daure hannunsa a matsayin hukunci, Buba ya zargi kansa da daukar doka a hannunsa “Yaron ya sace wayar dana sai wani mutum ya kama shi aka kawo shi gida, muka daure shi a gida tun daga 1:30 har zuwa lokacin da aka sakko daga Sallar jumma’a.
Muka bar yaron a daure a gida. Kuskuren da na yi shi ne lokacin da aka kawo mini yaron, na dauki doka a hannuna maimakon in nemo hanyar da ta dace,” kamar yadda ya zargi kansa.
Da yake karin haske game da irin hukuncin da aka yi wa Adamu, Buba ya ce, “Da farko na yi niyyar kwance shi kafin in tafi Sallah amma saboda ina da shakkar yaron zai gudu shi ya sa na bar shi daure da misalin karfe 1:30 na rana, ban kwance shi ba sai misalin karfe 2:15 na wannan rana. Shirina shi ne in kai shi sashen ‘yansanda na Kashere, amma hakan ya gagara saboda fushina.
Yayin da ya yaba da kokarin jami’an tsaron Nijeriya da jami’an tsaron NSCDC na shiga cikin lamarin,
“Iyayen (Adamu) wanda aka abin ya faru da shi, bayan sun ji abin da ya faru da dansu, sun kai karar ofishin hukumar tsaro ta Cibil Defence suna neman hakkin dan nasu kuma dole ne a hukunta ni. Amma da na isa ofishin, sai aka ce in fara biyan Naira 30,000 na jinyar yaron kuma in sa hannu a kan cewa zan dauki alhakin duk abin da zai faru da yaron nan gaba.
“Na biya kudin, sannan dan uwana (mahaifin Adamu) ya karbi kudin ya tafi, kuma na ci gaba da biyan kudin jinyar yaron duk da na biya Naira 30,000 na farko.
“Ina so in gode wa NSCDC saboda yin la’akari da lamarin. Duk da cewa suna tuhuma ta amma sun yi kokari sosai wajen gyara lamarin.
“Watakila da a ce sun shiga lamarin tun da farko da ba a kai ga yanke masa hannu ba, amma dai sun tabbatar da lafiyar yaron, sun sanya hannu a kan duk takardun da suka dace don ganin yaron ya samu kyakkyawar kulawa,” in ji Buba.
Ya ci gaba da jaddada cewa, “Duk da haka, jami’an NSCDC, sun tabbatar da cewa Adamu ya samu mafi kyawun kulawar jinya,” in ji shi.
Adamu, wanda ya musanta zargin kawun nasa, ya ce a tarinisa bai taba sata ba.
Da aka tuntubi mahaifin Adamu, Tela Daji, ya musanta zargin da Buba ya yi masa na yin almubazzaranci da kudin da aka tanadar domin jinyar dansa.
“Yayana yana kokarin nemo wanda zai zarga da yadda zai wanke kannsa a cikin lamarin.
“Ban dauki wani kudi da aka tanadar ba. Hasali ma lokacin da aka bayar da Naira 100,000 ba ni ne aka ba wa. NSCDC ce ta kasance mai kula da harkar maganin, ban taba barin wurin da dana yake ba,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Hukumar NSCDC ta fara tuhumar Buba da laifin aikata laifuka, kamar yadda ta yi alkawari a wata hira da Kwamanda Muhammad Bello, da wakilinmu.
Sai dai bisa ga bayanan kotu da Arewa PUNCH ta samu, an dakatar da shari’ar saboda Buba ba shi da wakilci a shari’ar.
Mai shari’a Durabo Sikam na babbar kotun Gombe a ranar 9 ga watan Yuli ya sanya ranar 8 ga watan Yuli domin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Magatakardar Kotun, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “Dalilin da ya sa aka dakatar da shari’ar a halin yanzu shi ne saboda wanda ake kara (Buba) ya bukaci kotu da ta ba shi wasu kwanaki domin ya samo lauyan da zai kare shi.