An wallafa makala mai taken “Kafa kyakkyawar makomar huldar Sin da Tajikstan cikin hadin kai”, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping da ke ziyarar aiki a kasar Tajiskstan ya rubuta, a yau Juma’a a kasar ta Tajikstan.
Xi Jinping ya bayyana cikin makalarsa cewa, a halin yanzu, Sin da Tajikstan na cikin wani muhimmin mataki na raya da kuma farfado da al’umma, sa’an nan yana mai fatan yin tattaunawa da takwaransa na kasar Tajikstan Emomali Rahmon don gaggauta raya huldar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
A yayin ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Tajikstan, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG zai gabatar da shiri a harshen Tajikstan mai taken “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” a zagaye na 3, inda kafofin yada labarai da dama sun ba da labarai kan wannan batu, lamarin da ya jawo hankalin bangarori daban-daban na kasar. (Amina Xu)