Majalisar Wakilai ta fara bincike kan zargin karkatar da Naira biliyan ₦1.5b da manyan jami’an ma’aikatar mata ta tarayya suka yi wa ‘yan kwangila. Wannan bincike da kwamitin majalisar kan harkokin mata ya jagoranta, ya biyo bayan koke-koke ne daga ‘yan kwangilar da suka ce ba a biya su kwangilar da aka kammala ba.
Shugaban kwamitin, ‘yar majalisar wakilai Kafilat Ogbara, ta bayyana cewa ma’aikatar ta bayar da sabbin kwangiloli a jihohi 15 da ba a saka su a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 ba, inda aka karkatar da kuɗaɗen da aka tanada domin tsofaffin ‘yan kwangila.
- An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi
- An Jinjinawa Matakan Kare Hakkin Bil Adama Na Kasar Sin Yayin Zaman Taron MDD
Mista Aloy Ifeakandu, Daraktan kuɗi da gudanarwa a ma’aikatar, ya ce ya bi umarnin hukuma kuma akwai bayanan da suka dace.
Babban Sakataren dindindin, Gabriel Aduda, ya bayyana cewa kashi 25% na kasafin kuɗin ma’aikatar Naira biliyan ₦13.6b na shekarar 2023 ne kawai aka saki, inda ba a fitar da ragowar Naira biliyan ₦10.2b ba.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC tana kuma binciken ma’aikatar kan Naira biliyan ₦1.5b da aka fitar daga watan Nuwamba da Disamba 2023. Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya tabbatar da cewa an saki Naira biliyan ₦1.5b ga ma’aikatar.
Kwamitin ya gayyaci ministar harkokin mata Uju Kennedy-Ohaneye da ta bayyana a ranar 9 ga watan Yuli, kuma ta bayar da umarnin dakatar da duk wasu ayyukan kwangilar a shekarar 2024 har sai an warware matsalar.