Saudiyya ta yanke wa wani malamin makaranta, Asaad al-Ghamdi mai shekaru 47 hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari saboda sukar gwamnati a shafukan sada zumunta.
An kama shi a watan Nuwamban 2022 a birnin Jeddah, kuma aka yanke masa hukunci a ranar 29 ga Mayu a wata kotu ta musamman, inda aka zarge shi da ta’addanci.
- Kaf Nijeriya Cikin Filayen Jiragen Sama Fiye Da 22, 3 Ne Kacal Ake Cin Riba – FAAN
- Fakewa Da Batun Kasar Sin Ba Zai Taimaka Wa NATO Cimma Burinta Da Ya Shafi Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba
Takardun kotu sun nuna cewa an tuhumi Ghamdi da “kalubalantar addini da adalcin Sarki da Yarima” da “wallafa jita-jita da labarun karya.”
Shaidun da aka gabatar sun haɗa da rubuce-rubucen da ya suka soki ayyukan ‘Vision 2030’ da nuna alhininsa ga mutuwar dan gwagwarmaya Abdallah al-Hamed.
Lamarin Ghamdi ya yi kama da na dan uwansa Mohammad, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bara saboda yada wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.
Dan uwansu na uku, Saeed, wanda malamin addini ne da ke gudun hijira, ya yi Allah-wadai da hukuncin, inda ya ce babu komai game da tuhume-tuhumen face zalunci.
A cikin ’yan shekarun nan, kotunan Saudiyya sun yanke hukuncin daurin shekaru masu tsawo ga mutane da dama saboda rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta, ciki har da Nourah al-Qahtani da aka yanke wa hukuncin shekara 45 da Salma al-Shehab da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 34.
Akwai Manahel al-Otaibi, wadda aka yanke wa hukuncin shekara 11 saboda kalubalantar dokokin Saudiyya game da sanya sanya abaya ga mata.