Kamfanin Jirgin Ƙasa na Nijeriya (NRC) ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba makiyaya da ‘yan kasuwa za su ci gaba da amfani da jiragen kasa wajen jigilar shanu da kayayyaki daga Arewa zuwa Kudu.
Daraktan NRC, Fidet Okhiria ne, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
- Emefiele Ya Yi Amfani Da Wakili Wajen Karbar kwangila Daga CBN – Shaida
- Kaf Nijeriya Cikin Filayen Jiragen Sama Fiye Da 22, 3 Ne Kacal Ake Cin Riba – FAAN
Okhiria ya ce jirgin da zai ci gaba da jigilar shanu da sauran kayayyaki na kan hanyar shirya fara aikinsa.
A 2017, NRC ta daina jigilar shanu a jirgin kasa saboda matsalolin da suka mamaye sufurin jirgin kasa.
Ya ce hukumar na sa ran nan da wata daya ko biyu, makiyaya za su iya fara amfani da jirgin kasa a Warri zuwa Itakpe.
Ya kuma ce hukumar ta zamanantar da sufurin kayayyaki a jiragen kasa don saukaka wa mutsne.
Wannan yana nufin shanu da sauran kayayyaki za su tashi daga Arewa ta jirgin kasa zuwa Warri a yankin Kudu Maso Kudu.
Hukumar NRC ta kawo sabbin taragon jiragen kasa da za su ke aikin jigilar dabobbi da sauran kayayyaki.