A ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2012, Xi Jinping wanda ya hau kan mukamin babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a watan Nuwamban shekarar, ya ziyarci lardin Guangdong, inda ya bayyana cewa, “yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje muhimmin aiki ne da aka sa gaba, wanda ke da babbar alaka da makomar Sin”, kuma ya ba da umurnin karfafawa dukkan mambobin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato JKS da al’ummun kasar gwiwar “kara yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ba tare da tsayawa ba”. Xi Jinping ya ce, “Shawarar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, nagartaccen mataki ne mai dacewa, dole ne mu nace ga wannan hanya a nan gaba, wadda za ta kawo wadata ga kasa da al’umomminmu.”
A shekarar 2013, a gaban dimbin mabambanta kalualoli masu tsanani da ake fuskanta a cikin gida da kuma waje, Xi Jinping ya tantance yanayin da ake ciki, ya yanke shawarar zurfafa yin kwaskwarima a kasar, ta yadda za a tabbatar da ganin kasar Sin ta samu ci gaba yadda ya kamata. Xi ya ce, “Kasar Sin ta shiga muhimmin lokaci na magance kalubaloli mafi tsanani da ya kamata a daidaita su ta hanyar kara yin kwaskwarima. Dukkansu matsaloli da kalubaloli ne da za a sha wahaloli matuka wajen daidaita su.”
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- Tsaro Da NATO Take Magana Ya Dagora Ne Kan Salwantar Tsaron Sauran Mutane
Baya ga hakan a shekarar 2018, Xi Jinping ya sake daukar matakan yin kwaskwarima mai karfi sosai kan hukumomin jam’iyyar JKS da na gwamnatin kasar. Wannan mataki ne mafi kasaita da aka dauka bayan aka kaddamar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a shekarar 1978, wanda ya ba da tabbaci ga manufar kara yin kwaskwarima a cikin gida a hukumance.
Kazalika a bana, gabanin budewar cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwamins ta Sin na 20, Xi Jinping ya gabatar da jigon taron, wato “Zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni bisa jigon zamanintar da al’ummar Sin”, abin da ya ba da wani sako cewa, wannan aiki na yin kwaskwarima, ya shiga wani sabon muhimmin mataki. (Amina Xu)