Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina ta zargin tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma ministan Babbar Birnin Tarayyar Abuja, Nyensom Wike da zama kanwa uwar gamin hana jam’iyyar zaman lafiya.
Daraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2023 kuma jigo a PDP, Mustapha Inuwa ne ya bayyana hakan a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya gudana a Katsina.
- CAF 2025: Nijeriya Ta Fito A Rukuni Mai Zafi
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Haka kuma jam’iyyar ta ce duk inda ake samun wata rashin fahimta a jihohi da kuma kasar baki daya, to tsohon gwamnan Jihar Ribas ne musabbabi.
Mustapha ya kara da cewa irin yadda aka hana wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP su sayi fom din takarar shugabancin jam’iyyar da ke tafe ya nuna cewa akwai masu mata zangon kasa daga matakin tarayya.
A cewarsa, abin ya fito fili lokacin da tsohon gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya bayyana cewa shi da Wike ba su da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, sai Tunibu a matsayinsu na ‘yan jam’iyyar PDP.
“Hakan ta sa suke tura mutanen su duk inda za a yi zaben shugabannin jam’iyyar PDP domin su kawowa jam’iyyar cikas a lokacin zabe mai zuwa, kuma shi ne abin da suke kokarin cimmawa.
Idan za a yi tunawa jam’iyyar PDP a Jihar Katsina tana fama da rikici tun bayan kammala zaben 2023, inda har yanzu ana ci gaba da samun matsaloli abin da wasu ke ganin cewa Wike ne kanwa uwar gamin wannan matsala.
Haka kuma wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar a Jihar Katsina sun zargin tsohon dan takarar gwamna a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado DanMarke da yin uwa makarbiya kan lamurran jam’iyyar PDP.
Kazalika, Sanata Yakubu na biyayya ne a bangaren Wike. Yanzu dai ana jira a gani lokacin zaben shugabannin jam’iyyar PDP da ke tafe me zai faru