Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai ƙaddamar da shirin lamunin ɗalibai a ranar Laraba, 17 ga Yuli, 2024, a fadar Shugaban Ƙasa, da ke Abuja. Kaddamarwar zai kasance alamar fara aiwatar da shirin, wanda aka tsara domin bayar da tallafin kuɗi ga ɗalibai a faɗin Nijeriya.
A kwanan nan, Shugaba Tinubu ya amince da Naira biliyan ₦35b don farawa da shirin, wanda zai tallafawa ɗalibai 70,000 a shirin farko. Kwamitin gudanarwa na Asusun lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFund), wanda Mr. Jim Ovia ke jagoranta, ya amince da raba lamuni a taron farko da suka gudanar a Abuja a watan da ya gabata.
- Lokaci Ya Yi Da Nijeriya Za Rika Fitar Da Manja Kasashen Waje – Kungiyar Dalibai
- Buhari Zai Halarci Taron Tattaunawa Da Kungiyar Tuntuba Ta Katsina
A cikin wata sanarwa, NELFund ta jaddada muhimmancin wannan mataki wajen cika burinsu na tallafawa ilimi da ƙarfafa gwuiwar manyan shugabannin gobe.
Shirin lamunin dalibai wani shiri ne na musamman na gwamnatin Tinubu, da aka tsara don bayar da tallafin kuɗi domin kuɗin makaranta da alawus ga dalibai masu cancanta a duk faɗin kasar.
Fiye da dalibai miliyan 1.2m ake sa ran za su amfana daga wannan shirin a mataki na farko, wanda ke nuna jajircewar gwamnati wajen bunƙasa damar samun ilimi da kuma ƙarfafa cigaban shugabannin gobe a Nijeriya.