Gwamnatin Jihar Kebbi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta ƙaddamar da rabon takin noman damina ga manoma 48,000 a faɗin jihar kyauta.
A jawabinsa wajen taron, Gwamnan ya bayyana cewa “rabon takin, wata hanya ce na ƙara inganta samun wadataccen abinci a jihar da ƙasa da kuma kyautata rayuwar al’ummar jihar.”
- Majalisar Dokokin Kano Ta Samar Da Sabuwar Dokar Sarakuna Masu Daraja Ta Biyu
- Masu Horar Da Kongfu Na Sin Sun Taimakawa Nijar Horas Da ’Yan Wasan Da Za Su Halarci Gasar Olympics Ta Matasa Ta Dakar
Gwamna Nasir ya kara da cewa, rabon takin na daya daga cikin alkawuran da suka dauka yayin yakin neman zabe, inda ya yi alkawarin inganta harkokin noma da rayuwar al’ummar ta hanyar ba da tallafi da kuma gudanar da ayyukan jindadi da more rayuwar al’ummar jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kasafin Kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar, Dakta Abbas Sani Kalgo ya bayyana cewa” wannan bikin na yau shiri ne wanda za a raba taki ga manoman karkara na fadin jihar kebbi kyauta a karkashin shirin N-CARES wanda Gwamna Nasir ya kirkiro da nufin ingantawa da tallafawa Magidanta, Mata da Maza masu kananan sana’o’i, Ilimi da kiwon lafiya da sauransu.
Daga Karshe ya godewa Gwamna Nasir Idris kan irin kokarin da yake yi wajen ganin an inganta rayuwar al’ummar jihar da kuma samar da abinci.