Gwamnatin tarayya ta sanar da hana karɓar ɗaliban da ba su kai shekaru 18 ba zuwa manyan makarantu tun daga zangon karɓar ɗalibai na shekarar 2024. Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ne ya sanar da wannan a taron manufofin 2024 na Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB).
Farfesa Mamman ya bayyana cewa an sanar wa da JAMB wannan sabon tsari, wanda ke hana karɓar ɗalibai ƙanana zuwa jami’o’i da sauran manyan makarantu. Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na la’akari da shekaru 18 a matsayin mafi ƙanƙanta don shiga waɗannan makarantu domin tabbatar da shirye-shiryen ɗalibai ga ƙalubalen ilimi da na zamantakewa.
- Matsalolin Da Hukumar JAMB Ta Fuskanta A Jarrabawar Bana
- JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000 Da Suka Kammala Karatun Bogi
A cewarsa, wannan sauyi na manufofi yana da nufin inganta ƙimar ilimi da walwalar ɗalibai ta hanyar tabbatar da cewa waɗanda ke shiga manyan makarantu sun kai matsayin balaga don jure wa buƙatun karatu a matakin.