Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu da suka hada da Jami’oi, makarantu fasaha,kwalejin ilimin malamai, da sauran manyan makarantun kasa an kafa ta ne a shekarar 1978 shekaru 46 da suka gabata ke nan,wannan shine karo na 46 da hukumar take shirya irin jarabawar.
Mutum milyan ne 1,989,668 suka yi rajistar rubuta jarabawar ta wannan shekarar sai dai kuma milyan 1,904,189 ne suka rubuta jarabawar da aka yi kwan shida ana rubutawa, yayin da dubu 80,810 basu samu damar rubutawa ba.Hukumar ta yi amfani da wurare 700 wajen rubuta jarabawar ta bana a kowane sako da lungu na Nijeriya, inda aka fara rubuta jarabawar ranar Jumma’a 19 aka kammala ranar Litinin zuwa 29 Afrilu 2024.
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
- JAMB Ta Dakatar Da Wasu Jami’anta Saboda Tilastawa Wata Daliba Cire Hijabi
Farfesa Ishak Olanrewaju Oyelede shi ne shugaban hukumar na yanzu wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2016.
Wadanda suka fara rubuta jarabawar ranar Jumma’a sun bayyana yadda suka fuskanci matsaloli amma shugaban hukumar shirya jarabawa ta manyan makarantu Farfesa Ishak Oyelede,ya yi kira gare su cewar da su kwantar da hankalinsu,domin ya basu tabbacin hukumar za ta sake ware watarana ga su wadanda suka fuskanci matsalar a ranar.
Shugaban ya furta hakan ne lokacin da yake zagayawa domin wuraren da ake rubuta jarabarawar a Kogo-Bwari,babban birnin tarayya Abuja inda yace kamar yadda ya gani da idonsa jarabawar na gudana,ba tare da wata babbar matsala ba,in banda wuri daya da aka bada labarin an fuskanci wasu matsaloli.
Ya ce yana kara jan hankalin wadanda lamarin ya shafa su gane cewa babu makawa irin matsalolin sai sun faru,dole ne sai wasu wuraren rubuta jarabawar sun fuskanci matsaloli wajen yadda babu yadda ba za a samu damar rubuta jarabawar ba.Yana tunanin kamar wuraren rubuta jarabawar goma ne za su fuskanci irin matsalolin,saboda sun san irin kayan aikin da suke a wasu wuraren da irin ci gaban da ake da shi a wuraren.
“Ba son su bane irin hakan ke faruwa kamar yadda ya ce,ba amma idan ta faru sai dai a sa hakuri kar a yi kokarin yin abin da zai kara shiga matsala.
“In ana cikin rubuta jarabawa sai aka samu matsala dole ne a tsaya hakan ba zai bada dama a kawo wani sahun na masu rubuta jarabawa ba,dole ne abin ya tsaya a samu sanar da hedikwata.
Za a iya sake rubuta jarabawa ne bayan karfe hudu da rabi na yamma,wannan zai ba wadanda za su rubuta a jerin sahu na 2 da 3 kai har ma na 4 suna iya rubutawa,ta wani bangaren kuma ana iya barin rubutawa jarabawar kashe- gari.
Ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda wasu ke bada kyauta ga wadanda suka fi nuna hadaka lokacin jarabawar ba tare dayin la’akari da wadansu abubuwa ba,wadanda suke cikin wadanda ake dubawa lokacin da ake ba dalibai guraben karo ilimi na manyan makarantun.Kamar yadda ya kara yin bayani irin wannan tagomashin da ake yi bai dace ba.
Kamar kamafanoni irinsu”MTN da sauarn mutane suna bada damar karo ilimi ga wadanda suka fi samun maki lokacin jarabawar UTME,amma sai muka nuna masu cewar yin hakan bai dace ba,domin kuwa idan an samu maki mafi yawa a jarabawar shiga manyan makarantu,da akwai ma sauran abubuwan da suka kamata a duba su tukuna.Akwai maganar nagartar sakamakon jarabawar kammala sakandare sai an hada ta da sakamakon makin da aka samu a jarabawar.Maganar zuwa jami’ar sojoji ta NDA,can ma ai ana lura ne da yadda ake ganin jikin mutum a Zahiri, bayan an yi jarabawar kafin mutum ace a cancanci damar samun zuwa,ai bai dace a rika yin haka ba yin abubuwa a kudundune.
Ya ce sai ka saurari mutum yana maganar “Ai dana ya samu maki 330 bayan ya lashe jarabawar kamamala sakandare har darussa 7 duk da yabon da yafi dacewa na sakamako, ya kamata ko cancanta a bashi gurbin zuwa makaranta.Yana iya samun damar kamar yadda ya kara jaddadawa amma wannan sai dai a kauyensu,amma idan ana maganar Nijeriya ne tana iya yiyuwa sai ya samu 650 duk da kwazon da shi mahaifin shi yake ganin yana da shi.
Hukumar shirya jarabawar manyan makarantu ta kasa ta ce za ta fara bada sakamakon jarabwar tun daga ranar 2 ga Mayu 2023,wannan bayanin yana dauke ne a matakan da aka dauka lokacin da aka yi taron gaggawa na hukumar,makon daya gabata a Abuja.Bayanin hakan yana dauke ta jawabain bayan taron d a aka rabawa ‘yan jarida rana r Litinin ta hannun jmi’an yada labaran hukumar Dakta Fabian Benjamin.
Hukumar ta bada dalilan da suka sa ba a bayyana sakamakon jarabawar da wuri ba,domin a tabbatar da duk matakan da suka kamata an dauke su kafin akai ga yin hakan.
“Yayin da wadanda suka rubuta jarabawa z su fara duba sakamako ranar Talata 2 ga Mayu 2024, wadanda suka rubuta jarabawa amnma sun fuskanci matsaloli ba tare da sun sani ba,ba za su ga sakamakon su ba, maimakon haka za su ga sanarwa ta sake duba jarabawa ranar Asabar 6 ga Mayu 2023.