• English
  • Business News
Friday, June 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zanga-Zanga: Ba A Gyara Barna Da Barna

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
in Labarai, Siyasa
0
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwanan nan batun zanga-zangar da matasa ke yekuwar yi a fadin Nijeriya zuwa karshen watan Yulin da muke ciki ta dauki hankulan al’umma. Malamai, masana da sauran jama’a kowa yana ta tofa albarkacin bakinsa a game da manufar zanga-zangar, wadanda suka kudiri aniyar yi (matasa) da ita kanta zanga-zangar ma.

Ya ku ‘yan uwana ‘yan Nijeriya ku sani: duk irin tsananin halin da muke ciki, wallahi gwara hakan da a ce kasar mu ta yamutse, ta shiga tashin hankali, fada ya barke. Misali, yanzu kasashe irin su Sudan, Syria, Yemen da sauransu, wallahi duk sun gwammace a ce suna cikin irin halin da muke ciki a Nijeriya, da irin yanayin da suka fada na damuwa da yaki da tashin hankali. Don haka matasa a yi hattara, kar mu yarda da duk wanda zai zuga mu mu yi tashin hankali, ko mu kara jefa kasar mu cikin wata damuwa!

  • Ba Za Mu Shiga Zanga-zangar Da Za A Yi Wa Tinubu Ba – Daliban Arewa
  • Zanga-Zanga Ko Kun San Babban Dalilin GarÆ™ame Abusalma A Kurkuku

Haba ‘yan uwana matasa, to ko a kasashen Turai, inda zanga-zangar ta samo asali, wa ya fada maku cewa duk lokacin da aka yi zanga-zanga sai shugabanni sun yi abin da ake so? Kwanan nan wace irin zanga-zanga ce ba a yi ba a kasashensu, a kan irin cin zalin Falasdinawa da isra’ila take yi, kuma gwamnatocinsu suna bai wa isra’ila makamai? Amma don Allah sun daina abun da suke yi na goyon bayan Isra’ila?

A nan Nijeriya da aka yi zanga-zangar ‘EndSars’ a kasar nan, a kan cin zalin ‘yan sanda, ai an kashe mutane da yawa, an kona dukiyoyi masu tarin yawa, kuma an fasa gidajen yari ‘yan ta’adda da yawa sun fito, sun gudu, sun addabi mutane, amma abin da aka nema na hana cin zalin ‘yan sandan yana nan bai gushe ba. To meye amfanin zanga-zangar kenan? Shin ‘yan Nijeriya don Allah ba za mu hankalta ba?

Tun daga shekarar 2011 dukkanin kasashen da suka yi zanga-zanga wai da sunan zaluncin shugabanni, da wadanda suka yi nasarar kifar da shugabannin, da wadanda ba su yi nasara ba, babu wadanda ba su ce gara jiya da yau ba, babu wadanda zanga-zangar ta warware wa matsalar da suke ciki a kasashensu, duka matsalolin da ake kuka a kan su, wallahi suna nan, kuma zanga-zangar ma ta zo da wasu matsalolin na daban wadanda kafin ta ma babu su. Shin ‘yan Nijeriya ba za mu hankalta ba?

Labarai Masu Nasaba

Leicester City Ta Sallami Ruud van Nistelrooy A Matsayin Kocinta

Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

Duk wanda ka ga yana tattauna hukuncin zanga-zanga a addini, idan ka ga ya siffantu da sifa biyu, to ka sani dan son zuciya ne, ba gaskiya yake so ba, siffofin su ne kamar haka: Idan ka ga baya kawo maka Hadisan da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya hana a yi fito-na-fito ga shugaba saboda wani aikin assha da yake yi, har Hadisin ya siffanta wanda ya mutu a hakan a matsayin wanda ya yi mutuwar jahiliyyah, da Hadisan da suke hana yi wa shugaba nasiha a fili sai a boye.

Na biyu, iIdan ka ga yana kafa maka hujja da abubuwan da suka faru na fitintinu a tsakanin sahabbai, wanda abu ne sananne cewa: ba a sanya cin karo tsakanin maganar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam da aikin wani, ko da kuwa sahabi ne, ballantana abubuwan da suka faru a lokacin fitina, wanda da yawan sahabbai sun kaurace masa saboda ba su gamsu da shi ba.

Masu zuga al’ummah su yi zanga-zanga da sunan addini ya ba da damar a yi, irin su Farfesa Labdo da makamatansa, ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood (Ikwanul Muslimin) da suka damalmala kasashen musulmai, muna fatan Allah ya shirye su, Allah ya kame hannunsu, ya kare al’ummah daga yaudararsu da sharrin da suke yadawa, amin.

Akwai abubuwan da duk mai hankali ba sai an ce masa kar ya yi ba, saboda bayyanar tasirin barnarsu a fili karara, da izina da aka samu kansu, koda wasu gafalallu suna ingiza mutane da suyi!

Mai hankali yana daukar izina ne daga waninsa, ba ya bari ya zama abin daukar izina!

Daga cikin illar zanga-zanga a kasar nan, hatta jami’an tsaron da muke ta kukan sun yi kadan, wadanda suke cikin daji wajen yakar ‘yan ta’adda, da wadanda suke kan manyan hanyoyi, idan har aka fara wannan zanga-zangar ta tsiya, duk hankalin gwamnati zai dawo wajen shawo kan zanga-zangar, a manta da maganar tsaro da ‘yan ta’adda, wanda hakan zai yi mummunar illah ga sha’anin tsaron kasar nan.

Allah yasa mu gane, Allah ya shiryar da mu, amin.

YA KU ‘YAN UWANA ‘YAN NIJERIYA, SHIN ANYA DA GASKE MUNA SON INGANTACCEN SHUGABANCI A KASAR MU KUWA?

Ni dai a iya bincikena, da iya yawon da na yi a duniya, ban taba ganin masu kukan zaluncin shugabanni, kuma wadanda ba da gaske suke yi ba, kamar ‘yan Nijeriya. Dalilai na su ne kamar haka:

  1. Duk wanda ka ga yana kukan ana zalunci, to mafi yawa bai samu damar a yi zaluncin da shi ba ne, ko kuma da aka yi zaluncin ba a dan sammasa ba ne, ba wai tsabar kyamar zaluncin ba ne da gaske ya sa muke ta ihu. Da zarar an shigar da mutum ciki, to za ka ji ya yi shiru, watakila ma har kare abin zai rika yi, iya in da karfinsa ya kare.
  2. Duk kukan da ake yi na rashin ingancin shugabanci, idan zabe ya zo, wadannan da ake kuka a kansu, idan sun bayar da atamfa ko taliya, ko kuma sun raba wasu ‘yan kudade, sai ka ga su ake zabe ba wadanda suka cancanta ake zabe ba.
  3. Babu wanda ke son a fada masa inda tasa matsalar take domin ya gyara, kowa so yake a ce matsalar Nijeriya ta wasu ce ba tashi ba ce.

WATA KILA SABODA BA DA GASKE MUKE YI BA, SHI YA SA KA GA ALLAH YA KYALE MU MUKA SHIGA HALIN DA MUKE CIKI A YAU.

Amma gaskiyar magana, wallahi laifin ba na shugabanni kawai ba ne. Dukkaninmu, kowa ya duba laifinsa, mu gyara, sai Allah ya tausaya muna.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Zanga-zanga
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jakadar Sin A Nijar Ya Halarci Bikin Bude Gasar Dambe Ta Nijar Karo Na 6

Next Post

Gyare-Gyaren Da Sin Ke Yi Zai Samar Da Karin Moriyar Bude Kofa Ga Duniya

Related

Leicester City Ta Sallami Ruud van Nistelrooy A Matsayin Kocinta
Siyasa

Leicester City Ta Sallami Ruud van Nistelrooy A Matsayin Kocinta

2 hours ago
Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki
Manyan Labarai

Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

3 hours ago
JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don ÆŠaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa
Ilimi

JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don ÆŠaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa

4 hours ago
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka
Manyan Labarai

Ganduje Ya Ajiye Shugabancin Jam’iyyar APC

5 hours ago
Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS
Labarai

Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS

8 hours ago
Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson
Siyasa

Zaɓen 2027 Ya Fi Damun Tinubu Fiye Da Gudanar Da Shugabanci – Sanata Dickson

9 hours ago
Next Post
Gyare-Gyaren Da Sin Ke Yi Zai Samar Da Karin Moriyar Bude Kofa Ga Duniya

Gyare-Gyaren Da Sin Ke Yi Zai Samar Da Karin Moriyar Bude Kofa Ga Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

June 27, 2025
Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

June 27, 2025
Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17

Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17

June 27, 2025
Leicester City Ta Sallami Ruud van Nistelrooy A Matsayin Kocinta

Leicester City Ta Sallami Ruud van Nistelrooy A Matsayin Kocinta

June 27, 2025
Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko

Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko

June 27, 2025
Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

June 27, 2025
Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba

Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba

June 27, 2025
JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don ÆŠaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa

JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don ÆŠaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa

June 27, 2025
Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai

Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai

June 27, 2025
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (7)

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (7)

June 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.