Gwamnatin jihar Naija za ta haramta sana’ar karuwanci a Minna, a wani bangare na kokarin magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar.
Babbar Sakatariya a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Kaltum Rufa’i, ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Minna.
- MajalisaTa Amince Da Dokar Kafa Hukumar Yaki Da Yaduwar Makamai
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Tsaro Da Zaman Lafiya Tsakaninta Da Afrika
Ta ce gwamnati ba ta da masaniya kan irin wadannan ayyuka marasa kyau da za su iya kara ruruta wutar kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.
Ta ce akwai dokokin jihar da suka haramta irin wannan sana’a, tana mai cewa gwamnati za ta yi bincike da nufin dakatar da wannan ta’ada a jihar.
“Yanzu da kuka kawo mana maganar, gwamnati za ta fara aiki. Ni da kaina zan je na gana da Sakataren Gwamnatin Jiha don tattaunawa kan lamarin da kuma nemo mafita,” in ji ta.
Binciken da NAN ta gudanar a Minna, ya nuna cewa manyan mata da ‘yan mata na fara sana’ar ta su ne daga karfe 7 na dare zuwa tsakar daren kowace rana.
Mafi kyawun wuraren da su ka fi tsayawa domin jan hankalin kwastomomi a babban birnin sun hada da shatale-talen City Gate, sai kuma hanyar zuwa titin NNPC.
Wasu jihohi na arewacin Nijeriya sun sha kafa ko haramta irin wannan sana’a don gudun tabarbarewar tarbiyya ko kuma rashin tsaro.