Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta musanta rade-radin cewa ta janye daga zanga-zangar kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, NLC ta bayyana rahotannin a matsayin karya tare da cewa ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ita ta shirya ba.
- Gwamnati Ba Za Ta Yi Amfani Da Karfi Ba Akan Masu Zanga-zanga – Minista
- Shugaba Tinubu Masoyin Arewa Ne – Gwamna Uba Sani
“Masu shirya zanga-zangar ta kasa ce kawai za su iya yanke shawarar janyewa ko ci gaba da zanga-zangar,” in ji NLC.
Sanarwar ta bayyana cewa “NLC tana da hanyoyi musamman hanyoyin yanke hukunci kan jagoranci wanda ayyukanta na masana’antu kamar zanga-zangar ke bi kafin a gudanar da irin wadannan ayyukan.”
NLC ta kuma nuna goyon bayanta ga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa, tare da amincewa da matsin tattalin arzikin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.
“Kasancewar NLC da cewa ba ita ta shirya zanga-zangar ba, hakan ba ya nufin kungiyar ta manta da halin kuncin rayuwa da ‘yan Nijeriya ke ciki sakamakon munanan manufofin tattalin arziki na gwamnati,” in ji kungiyar ta NLC.
NLC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tattaunawa da jagororin zanga-zangar domin biyan bukatunsu inda ta ba da shawarar a guji amfani da karfi wajen mayar da martani ga rashin jin dadin jama’a.
Tuni dai shugaban na Nijeriya ya roki ‘yan kasar da su janye shirin zanga-zangar da suke niyyar yi a farkon watan Agusta mai kamawa.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar gwamnati a Abuja bayan kammala ganawarsa da shugaban kasar.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ita su jira su ga matakin da zai ɗauka a kan korafe-korafensu.
Rokon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a fadin kasar musamman ma a shafukan sada zumunta.