A halin yanzu Nijeriya da kasar Amurka sun jaddada shirin kara karfafa harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakaninsu.
Wannann ya biyo bayan taron koli nena kasashen da ya gudana a tsakanin Ministar Masa’anatu, Kasuwanci da Zuba Jari na Nijeriya, Dakta Doris Uzoka-Anite, da tawagar kasar Amurka a karkashin jagorancin mataimakin sakatare mai kula da harkokin ciniki da kasuwanci tsakanin kasashen waje, Mista Arun Benkataraman, a Abuja ranar Laraba.
- Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Na Shirin Shiriricewa
- Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
Taron ya mayar da hankali ne wajen karfafawa tare da tabbatar da yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu da suka hada da shirin nan na (TIFA) da (AGOA) da (BNC) da kuma (CID) wadanda ke karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika da duniya baki daya ba a manta da su ba.
Duka bangarorin sun karfafa bukatar fadada harkokin kasuwanci a tsakaninsu tare da kuma kirkiro da sabbin hanyoyin cimma bukatun kasashen nasu domin bunkasa tattalin arzikin juna.
Dakta Uzoka-Anite ta bayyana abubuwan da Amurka za ta amfana dasu a Nijeriya wadanda suka hada da kasancewar ta babbar kasuwar da babu irinta a nan kusa da kuma ma’adanai da Allah ya hore mana a sassan kasa, haka kuma muna da kwararru masu ilimi daban-daban da za a iya fitar dasu zuwa kasashen waje su amfanar da kasashe daban-daban,” in ji ta.
Ta kuma jinjina wa dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka. “Nijeriya da Amurka sun dade suna hulda da juna na tsawon shekaru, suna mutunta juna tare da amfanar juna a bangarorin tattalin arziki da dama,” in ji ta.
A nasa jawabin, Benkataraman ya sanar da goyon bayan Amurka ga shirin farfado da tattalin arzikn kasa da kuma irin kalubalen da kamfanonin Amurka da ke harkoki a Nijeriya ke fuskanta.
“Za mu yi aiki domin karfafa dangantakar da ke tsakanin mu domin samun ci gaba da bunkasar tattalin arziki ta yadda al’ummar kasashen biyu za su amfana,” in ji shi.
Tawagar ta kasa Amurka ta nuna sha’awarta ga sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu take yi, sun kuma yi alkawarin bayar da gudummawarsu wajen karfafa kasuwanci da zuba jari a Nijeriya a daidai wannan lokacin.
Duka bangarorin sun amince da ci gaba da tattaunawa akai akai tsakaninsu don tabbatar da dorewar yarjejeniyar da aka kulla. An kammala taron tare da alkawarin kara karfafa kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.