Masana tattalin arziki sun yi kira ga gwamnati da ta rage harajin da ake dora wa kananan masana’antu domin su samu damar biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 da gwamnati ta cimm a yarjejniyar ta da kungiyar kwadago a kwanan nan.
Farfesa Akpan Ekpo, malami a jami’ar Uyo, ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin.
- Manchester City Na Buƙatar Yuro Miliyan 77 Kafin A Ɗauki Ɗan Wasan Gabanta
- Ƴancin Gashin Kai: Gwamnati Ta Gargadi Ƙananan Hukumomi Kan Kashe Kuɗaɗensu
Ya kara da cewa, ya kamata a tsame manyan kamfanonin da suke da karfin biya wannan sabon mafi karancin albashi daga wannan tsari na rage haraji.
Ya lura da cewa, hanya mafi sauki da gwamnati za ta taimaka wa bangaren kamfanoni masu zaman kansu daba za su iya biyan mafi karancin albashi ba shi ne na rage musu haraji.
“Saukin da kananan masana’antu za su samu shi ne na rage musu haraji domin yana da wahala a ce gwamnati za ta basu wani tallafi na kudi, amma yana da matukara sauki a rage musu haraji na wani lokaci,” in ji masananin tattalin arzikin.
Ya kuma bayar da hujjar cewa, a halin yanzu masu kananan masana’antu na fuskatar matsaloli da dama ciki har da na rashin daidaiton kudaden kasashen waje da rashin tsayayyen wutar lantarki.
Ya ce, in har ba a samu bayar da wannan tallafin ba akwai yiwuwar a samu rashin ayyukan yi da karin marasa ayyuka a kasa saboda za a iya koran ma’aikata a daga bakin aikinsu.
Haka kuma wani masanin tattalin arziki mai suna Mista Dr Muda Yusuf, a tattaunawarsa da manema labarai ya amince da matsayar Farfesan ya kuma ce, yanayin da ake ciki a halin yanzu baya taimaka wa bangaren masu masana’antu masu zaman kansu a Nijeriya a saboda haka ya bukaci gwamnati ta samar da hanyoyin taimakawa masa’anantu domin su samu cimma biya wannan mafi karancin albashin.
Idan za a iya tunawa, kungiyar masu masana’atu ta Nijeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta cika alkawarinta na tallafa wa masa’antu masu zaman kansu domin su iya biyan mafi karancin albashi na 70,000 da aka cimma da kungiyar kwadago a kasar nan.
Shugaban kungiyar, Segun Ajayi-Kadir ya yi wannan kiran ga gwamnatin inda ya ce wannan ne hanya mafi sauki da gwamnati za ta cika alkawarin ta.
A ranar 18 ga watan Yuli ne Shugaba Tinubu ya amince da Naira 70,000 matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan.