Wasu fusatattun matasa sun banka wuta sabon ofishin Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC a Jihar Kano.
Ofishin da ke titin zuwa gidan gwamnatin jihar da kuma karamar fadar da hambararren Sarki Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune.
- Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Abuja Zuwa Keffi
- Zanga-zanga: Kungiya Ta Gudanar Zanga-zangar Lumana A Jihar Filato
Tun da farko ‘yansanda sun tarwatsa wasu matasa da suka kunna wuta a kofar gidan gwamnatin Kano.
Daya daga cikin masu fafutuka da suka jagoranci zanga-zangar a Kano, Abba Hikima, ya bukaci ‘yansanda su shiga tsakani.