Masana a bangaren mai da iskar gas sun ce, umarnin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar a baya-bayan nan da ke umartar kamfanin samar da mai ta Nijeriya (NNPCL) da ta sayar wa matatar man Dangote danyen mai da naira ba zai kawo karshen matsalolin da matatar ke fuskanta a kowace rana ba.
Matakin na Tinubu dai na da manufar ganin an kawo karshen matsalolin da matatun mai na cikin gida ke fuskanta da kuma takun-saka da ake samu tsakanin NNPC da su kansu masu mamallakan matatun mai a cikin Nijeriya ciki har da matatar Dangote.
- Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa
- Bata-gari Sun Cinna Wa Sabon Ofishin NCC Wuta A Kano
A watannin baya, matatar man Dangote ta ci gaba da kokawa kan matsalar samun danyen mai da sauran kalubalen da take fuskanta a Nijeriya, lamarin da ta nuna barazana ga yunkurinta na kawo sauki ga al’umman Nijeriya a bangaren mai.
Hakan ya faru ne sakamakon yadda ta tunkari kasar Amurka da Burazil domin shigo da danyen man duk kuwa da cewa Nijeriya ce kasa mafi yawan danyen mai a dukkanin kasashen Afrika.
Matatar man Dangote ta zargi kamfanonin kasashen waje da ke Nijeriya da yin zagon kasa ga lamarin samar da danyen mai garesu. Daga baya kuma kamfanin ya shiga takaddama da hukumar kula da lamarin mai ta Nijeriya (NMDPRA) kan bin ka’idoji.
Hadimin shugaban kasa a bangaren yada labarai, Bayo Onaguga shi ne ya sanar da cewa, Tinubu ya umarcin kamfanin mai da yake sayar wa matatar man Dangote danyen mai a kan naira.
Onanuga ya ce an dauki matakin ne domin ganin an rage matsalar da ke akwai na musayar naira da dala.
Sa dai kuma, masana a bangaren sun nuna fargabar cewa duk da yunkurin na Tinubu, hakan ba zai kawo karshen matsalolin da matatar ke fuskanta ba.
Masanin harkokin mai, Barr. Ameh Madaki, ya yi amannar cewa umarnin Tinubu na sayar da danyen mai da naira ga matatar Dangote ba zai kawo karshen kalubalen da suke jibge ba.
Ya ce hakan ya faru ne sakamakon cewa Nijeriya ba ta da sauran ragowar danyen man da za ta iya sayar wa kowace matatar mai.
A cewarsa, danyen man Nijeriya kai tsaye ana sayarwa ne ga kwangilolin da suka fito daga wajen NNPCL kuma babu wani kari kan ganga miliyan 1.2 da kasar ke hakowa duk rana balle a yi maganar sayarwa ga wata matatar cikin gida.
Ameh ya ce, hanya daya kacal da za a samu sayar wa matatun man cikin kasar nan danyen mai shi ne, idan kasar ta kara yawan danyen man da take hakowa a kowace rana.
Kwararre a bangaren makamashi, Joseph Eleojo ya ce, “A ina ne kamfanin NNPCL zai samu danyen man da zai sayar wa Dangete da sauran matatun man cikin gida? Wannan shi ne shaidar da ya sa matatun man Nijeriya ba su aiki sama da shekaru 35.
“Matakin sayar wa matatar man Dangote danyen mai da naira, mataki ne mai muhimmanci kuma abun yawa ne, hakan zai rage wa matatun cikin gidan shan wahalar samun danyen man da za su sarrafa.
“Sai dai kar fa ‘yan Nijeriya su sa a ransu cewa farashin mai zai sauki idan har an sayar wa matatun cikin gida da danyen mai da naira.”
Kazalika, shugaban kamfanin harkokin makamashi na kasa da kasa, Dakta Diran Fawibe, ya ce, umarnin na Tinubu na sayar wa matatar mai danyen mai da naira zai taimaka sosai wajen inganta lamarin samar da mai a cikin Nijeriya.
Umarnin Shugaban Kasar Zai Ceto Wa Nijeriya Dala Biliyan 7.3 Duk Shekara – Adedeji
Babban Mashawarcin shugaban kasa kan haraji kuma shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta kasa (FIRS), Zacch Adedeji, ya ce matakin da Nijeriya ta dauka na sayar da danyen mai a kan naira zai ceto wa Nijeriya a kalla dala biliyan 7.3 a kowace shekara.
Adedeji wanda ya shaida hakan a ranar Litinin ya yin da ke bayyana alfanun umarnin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya bai wa kamfanin samar da mai ta kasa da cewar su sayar wa matatun cikin gida danyen mai a kan naira maimakon dala.
Ya ce a kowace wata, matakin zai taimaka wajen rage kashe kudaden waje da ya kai dala miliyan 660.
Shugaban FIRS, ya kara da cewa matakin na shugaban kasa zai rage wa Nijeriya dogara da musayar danyen mai wajen shigo da shi daga katare da kaso 30 zuwa 40 na kudaden da take kashewa.
A cewarsa, Nijeriya za ta iya tara rarar da ya kai kusan dala miliyan 7.3 da kuma rage wa kudaden da take kashewa duk wata a bangaren samar da man fetur da kusan kaso dala miliyan 660.
“A kowace wata, muna kashe kusan dala miliyan 660 wajen wadannan bangaren, sannan wannan mataki zai samar mana da rarar dala miliyan 7.92 kowace shekara,” ya shaida.
Idan za a tuna dai, Tinubu ya umarci kamfanin mai na kasa da ya dukufa wajen sayar da danyen mai ga Dangote da sauran matatun mai a kan naira maimakon dala. Yunkurin ya zo ne bayan takaddama da aka yi ta samu tsakanin matatar man Dangote da mahukuntan Nijeriya a bangaren mai.