Akalla mutum 6,900 da ake zargin mayakan Boko Haram ne kuma a halin yanzu za su fuskanci shari’a ta wucin gadi, a cewar gwamnatin Jihar Borno.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Zuwaira Gambo ce ta bayyana hakan a lokacin da ake kammala wani shiri na yada al’ada da koyo da Gidauniyar Zaman Lafiya Da Ci Gaba ta Allamin Foundation ta shirya a Maiduguri Babban Birnin Jihar Borno a ranar Talata.
- Masu Zanga-zanga Sun Fito Duk Da Dokar Hana Fita A Jigawa
- Manzon Musamman Na Xi Jinping Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Mauritania
A cewarta, kusan mutum 9,000 ne suka koma cikin al’umma, kuma shirin ya samu gagarumar nasara.
“Ya zuwa yanzu, kimanin ‘yan ta’addan Boko Haram 200,000 da iyalansu sun mika wuya ga gwamnatin jihar.
“Bari na fayyace, muna da mayakan Boko Haram na gaskiya kusan 6,900 a hannunmu, kuma za su fuskanci shari’ar wucin gadi saboda sun aikata laifuka. Muna aiki akan cewa; mayakan ne na gaske,” in ji ta.
Adalci kwarya wata hanya ce ta samar da zaman lafiya da ke neman magance abubuwan da suka gada na munanan laifuka da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula da ke faruwa a lokuta daban-daban, ciki har da ramawa, sulhu, gurfanar da su a gaban kotu, da yin afuwa.
Babbar Darakta ta Gidauniyar Zaman Lafiya Da Ci Gaba ta Allamin, Hamsatu Allamin, ta bayyana cewa mutanen da suka mika wuya sun yi nadamar alakarsu da Boko Haram.
A cewarta, sun bayyana nadamar kasancewarsu a cikin kungiyar ta’addancin, saboda rashin ilimi da kuma saukin yadda ‘yan tada kayar baya suka yi garkuwa da su.
“Idan ’yan Boko Haram sun yi amfani da akidarsu ta addini wajen wanke wa mutane kwakwalwa su shiga cikin su, mu ma mu yi amfani da addini mu fada musu gaskiya. Don haka, ina ba da shawarar cewa gwamnati ta yi amfani da addini don gyara wannan labari mai tayar da hankali,” in ji ta.
A karkashin shirin ‘Ginin sulhu: Hanyar da ta dace da al’umma don kawar da mata da ‘yan mata a Jihar Borno,’ an wayar da kan mata sama da 800 da aka zalunta kuma yanzu suna ba da gudummawa ga al’umma.
Ta kara da cewa “Sun shirya rungumar sabuwar rayuwa wacce ba ta da tashe-tashen hankula kuma su zama masu rike da madafun iko a cikin al’umma, tare da ba da gudummawa ga samar da zaman lafiya da ci gaban al’ummominsu baki daya.”