Kwanan nan ne ma’aikatar harkokin cikin gidan Amurka, ta fitar da kundin bayani na biyu na rahoton bincike kan “shawara game da gaskiyar abun da ya faru a makarantun kwana, na Indiyawan Amurka na tarayya”, rahoton da ya nuna cewa akwai yara ‘yan asalin wurin kusan dubu 1 a tarihi, wadanda suka rasa rayukansu lokacin da suke karatu, a makarantun kwana karkashin jagoranci, ko goyon-bayan gwamnatin Amurka, inda kuma aka azabtar da su, ko tilasta musu sauya addini, ko yi musu horo saboda magana da harshen uwa da suka yi, al’amuran da suka raunata su har abada.
A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya amsa tambayar da aka yi masa dangane da rashin yiwa Indiyawan Amurka adalci a tarihi, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi a fahimci wannan batu yadda ya kamata, kana, ya zama dole Amurka ta gyara kura-kuran da ta tafka a fannin keta hakkin dan Adam a duniya.
Wani labari na daban kuma ya ce, rahoton baya-bayan nan da kwamitin masana’antu da kasuwancin kasar Sin na kasar Australiya wato ACBC ya fitar, ya yaba da tasirin muradun kasuwancin da aka yi da kasar Sin ga iyalan Australiya. Game da hakan, Lin Jian ya ce, rahoton ya shaida babbar manufar dangantakar tattalin arziki, da cinikayya tsakanin Sin da Australiya, wato samun moriya da nasarori tare, har ma ya tabbatar da cewa, ci gaban kasar Sin dama ce ga Australiya, ba kalubale ba. (Murtala Zhang)