Gwamnatin Jihar Kano, ta sake sassauta dokar hana fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yammaci.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi wata gana wa da shugabannin tsaro a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata.
- Zanga-zangar Birtaniya: Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ‘Yan Nijeriya
- Zanga-zanga: Daga Tutar Rasha Cin Amanar Kasa Ne – Janar Musa
Idan ba a manta ba a ranar Juma’a ne, gwamnatin jihar ta fara sassauta dokar, ta hanyar bai wa Musulmi damar zuwa Masallacin Juma’a domin gudanar da ibada.
Daga bisani, a ranar Lahadi gwamnatin ta sake sassauta dokar daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana.
Wannan dai ya samo asali ne bayan da zanga-zangar yunwa ta rikiɗe zuwa tashin hankali a jihar.
Bata gari sun yi amfani da zanga-zangar wajen fasa shagunan mutane tare da lalata dukiyar gwamnati, wanda hakan ne ya sanya gwamnatin sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar Kano.