Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen daƙile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin Nijeriya. Shugaban ya ba da wannan umarni ne yayin wani taro a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda mahalarta kwas na 32 na Kwalejin tsaro ta ƙasa (NDC) suka tattauna kan damarmamakin da ke cikin sashen hakar ma’adinai wajen tallafawa tsaro da ci gaban ƙasa.
Tinubu ya jaddada muhimmancin samun hanyoyin tattalin arziki da dama, tare da nuna buƙatar kamfanonin haƙar ma’adinai su ba da fifiko ga lafiyar ƴan Nijeriya, musamman mazaunan wuraren da ake gudanar da ayyukan hakar.
- Fiye da Mata 50 Masu Haƙar Ma’adinai Sun Fuskanci Cin Zarafi a Jihar Nasarawa
- Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba: Nijeriya Na Asarar Naira Biliyan 9 Duk Shekara – Majalisa
Shugaban ya yaba wa mahalarta NDC kan binciken su mai zurfi, tare da lura da fahimtar su game da tasirin masana’antar haƙar ma’adinai ga zaman lafiyar ƙasa. Ya amince da ƙalubalen da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ke kawo wa, inda ya bayyana su a matsayin barazana da dole ne hukumomin tsaro su magance cikin gaggawa.
Tinubu ya kuma tabbatar wa tawagar goyon bayan gwamnatinsa wajen kammala ginin helkwatar NDC a Abuja, don ƙarfafa rawar da wannan cibiya ke takawa wajen tsara dabarun tsaron Nijeriya.
Kwamandan NDC, Rear Admiral Olumuyiwa Olotu, ya yaba da goyon bayan Shugaban ga kwalejin, tare da bayyana muhimman ayyukan ci gaba da aka samu a ƙarƙashin mulkinsa. Ya kuma nemi taimako wajen kammala ginin rukunin NDC na dindindin, wanda aka samu jinkirin kammala shi tun daga shekarar 2010.