Firayim Ministan Burtaniya Keir Starmer ya yi gargadi mai tsanani ga masu zanga-zangar ‘yan ra’ayin rikau, yana mai alkawarin wadanda ke da hannun a tarzomar Ingila mafi muni cikin shekaru 13 za su yi nadamar abin da suka aikata.
Zanga-zangar da aka fara ta auku ce bisa kisan wasu yara uku wacce ta bazu a fadin kasar.
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
- Yadda Aka Kashe Manoma 8 Da Sace Dabbobi 1,260 A Sakkwato
A Rotherham, Kudancin Yorkshire, masu zanga-zangar adawa da shigar bakin haure sun farfasa tagogi a wani otal da masu neman mafaka suke ciki.
LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa rikicin, wanda ya samo asali ne sakamakon rashin fahimtar da aka samu game da wani hari da aka yi a Southport, ya shafi garuruwa da birane da dama, wanda ya kai ga arangama tsakanin masu zanga-zangar da ‘yansanda.
Da yake jawabi ga al’ummar kasar ta gidan talabijin, Starmer ya ce, “Na ba da tabbacin za ku yi nadamar shiga cikin wannan matsalar. Ko kai tsaye ko wadanda ke yin wallafa bayanai ta intanet, sannan su gudu.” Ya yi Allah wadai da ‘yan daba kuma ya sha alwashin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Hotunan da aka watsa a BBC sun nuna yadda masu tarzomar suka tilasta shiga cikin Holiday Inn Edpress da ke Rotherham tare da tura wani abu da ke cin wuta a ginin. Har yanzu babu tabbas ko masu neman mafaka suna ciki a lokacin.
A Middlesbrough, daruruwan masu zanga-zangar sun fuskanci ‘yansandan kwantar da tarzoma, inda suka rika jifan jami’an, da duwatsu, gwangwani, da tukwane. An kama mutum sama da 90 bayan wata arangama da aka yi a wajen gangamin hannun dama a Liberpool, Manchester, Bristol, Blackpool, Hull, da Belfast.
Masu tarzoma sun yi ta jifan ‘yansanda duwatsu da kwalabe, inda suka jikkata jami’an da dama, kuma suka yi awon gaba da kayan shaguna da kona su, tare da yin kururuwa na kyamar Musulunci a lokacin da suke artabu da masu zanga-zangar. Rikicin dai shi ne mafi muni tun bayan tarzomar 2011 da ta biyo bayan kisan da ‘yansanda suka yi wa wani dan kabilar baki a Arewacin Landan.
Tiffany Lynch na hukumar ‘yansanda ta Ingila da Wales ya ce, “Yanzu muna ganin yadda matsala ta mamaye manyan birane da garuruwa.”
An fara tarzomar ce a Southport a daren ranar Talata bayan harin wuka da aka kai a ranar litinin a wani gidan rawa mai taken Taylor Swift. Wanda ake zargin, Adel Rudakubana mai shekaru 17, ana zarginsa da kashe yara uku tare da raunata wasu goma. Jita-jitar karya game da tarihinsa a shafukan sada zumunta ce ta haifar da tarzoma.
‘Yansanda sun danganta tashin hankalin da magoya bayan kungiyar kare hakkin bil’adama ta Ingila wato English Defence League da ke da alaka da kyamar kwallon kafa.
Masu tayar da kayar baya sun kai hari a akalla Masallatai biyu, lamarin da ya sa ma’aikatar harkokin cikin gidan Burtaniya ta ba da sabbin matakan tsaro na gaggawa ga wuraren ibada na Musulunci.
An dai shirya gangami a karkashin taken “Ya isa” a kafifin sada zumunta na dama. Mahalarta taron sun daga tutocin Ingilishi da na Biritaniya tare da rera taken “Dakatar da jiragen ruwa,” da ke nuni da bakin haure da ke tafiya Birtaniyya daga Faransa ba bisa ka’ida ba.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin Fascist sun gudanar da zanga-zangar adawa da shi a garuruwa da dama. A Leeds, sun yi ta rera wakar “Nazi sun kashe kan titunan mu” yayin da masu zanga-zangar dama suka amsa da “Ba Ingilishi ba ne kuma.”
Rahotanni sun nuna cewa ba dukkan tarukan ne suka koma tashin hankali ba. Wata zanga-zangar lumana a Aldershot an ga mahalarta rike da allunan da ke rubuta “Dakatar da mama.”
Gwamnatin Starmer dai na fuskantar jarrabawa tun farko wajen tunkarar tarzomar, bayan da aka zabe ta wata guda da ya gabata bayan da jam’iyyar Labour ta samu gagarumin rinjaye kan jam’iyyar Conserbatibes.
Kotu Ta Daure Masu Zanga-zangar Kyamat Baki A Burtaniya
A halin da ake ciki kuma, wata kotu a Birtaniya ta yanke hukuncin dauri kan wasu mutane da aka samu da laifin tayar da tarzoma tun zanga-zangar da ta barke sama da mako daya.
An yanke wa mutanen uku hukuncin shekara uku a gidan yari saboda shiga zanga-zangar a Liberpool.
Wannan ne matakin yanke hukunci cikin hanzari wanda gwamnati take son ya zama darasi, ya kuma dakile yiwuwar tashin hankali a gaba.
Rikicin na kin jinin ‘yan ci-rani ko baki shi ne mafi muni da ya bazu zuwa sassan Ingila da Arewacin Ireland.
An kama kimanin mutum 400 a garuruwa da dama.