Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a ranar Asabar, ya jaddada kudirinsa na yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
Ya bayyana haka ne a wajen bude taron karawa juna sani kan ka’idoji da dokokin yaki da cin hanci da rashawa ga daraktoci a jihar a Dawakin Kudu da ke karamar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano.
- Tsarin Shayar Da Jarirai Da Sauran Sauye-sauyen Da Aka Samu A Gasar Olympics
- Me Ya Fi Damun Matasan Nijeriya A Wannan Zamanin?
Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Gwarzo ya wakilta, ya ce, gwamnatinsa ta jajirce wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare don inganta walwalar jama’a.
A cewarsa, manufofin za su inganta jin dadin rayuwa da walwalar ‘yan jihar ta hanyar gudanar da mulkin dimokuradiyya na gari.
Amma wannan manufofin da tsare-tsaren ba za a iya cimmusu ba sai ta hanyar yakar cin hanci da rashawa ta kowace fuska.
Yusuf ya ce, gwamnatin da NNPP ke jagoranta ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba ta kowace irin hanya, don haka, ya bukaci dukkan daraktoci da su yi abin da ya kamata.
Shugaban Hukumar sauraren korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar, Alhaji Muhyi Gado, ya ce, taron bitar an yi shi ne da nufin bai wa daraktoci a ma’aikatun gwamnati ilimin yaki da cin hanci da rashawa.