A yayin da ake ci gaba da gudanar da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympic, abubuwa da dama suna faruwa a gasar ciki har da batun mata masu shayarwa da masu ciki da suka tsinci kansu a ci-kin gasar ta wannan shekarar.
Lokacin da ‘yar tseren yada-kanin-wani Aliphine Tuliamuk ta tashi zuwa gasar Olympics ta Tokyo a 2021, abu daya da yake a zahiri shi ne cewa ba za ta je sansanin gasar da ‘yarta ‘yar wata shida ba, mai suna Zoe.
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
- Sin Ta Ki Amincewa Da Duk Wanda Ya Yi Amfani Da Gasar Olympics Wajen Yada Yunkurin ‘Yan Aware Na Yankin Taiwan
A hirarta da manema labarai, ta ce “ Na yi kuka sosai a lokacin da aka dauke mu a motar bas zuwa san-sanin ‘yan wasa. Ba abin da nake yi sai kallon bidiyo da hotunan ‘yata. Da na isa sansanin ba na iya bacci ba tare da ita ba.”
Gasar ta kasance a lokacin da ake tsaka da annobar Korona, kuma gasar da Tuliamuk za ta yi za ta kasance ne a Birnin Sapporo na Arewacin Japan, kuma hakan na nufin Tuliamuk za ta iya kasancewa da iyalinta, sai dai kawai lokacin da ta kasance cikin damuwa shi ne, daren farko da ta kasance a sansanin da ‘yan gasar suka zauna a Tokyo inda aka haramta zuwa da yara.
Wannan ne dalilin da ya sa ‘yar tseren ta Amurka haifaffiyar Kenya ta yi maraba da tsarin da aka bullo da shi na barin mata masu shayarwa da masu kula da jariransu su halarci gasar Paris 2024, ciki har da samar da wani waje na yadda mata za su iya ganawa da jariransu a sansanin.
“Ina matukar farin ciki cewa cikin shekara hudu kawai daga lokacin da ba zan iya kasancewa da jaririyata ba, an samu sauyi inda yanzu za ka iya kasancewa da su. Wannan babban cigaba ne,” a cewarta
Batun lokacin da mace da ke gasar za ta daina shayar da jaririnta na daya daga cikin abubuwan da Tuliamuk, da ire-irenta suka yi fama da shi, hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bayar da shawarar bai wa jariri nonon uwa zalla tsawon wata shida na farko, sannan a ci gaba da shayar da shi hadi da isasshen abinci har zuwa shekara biyu ko sama da haka.
“Zan shayar tsawon wata uku ko hudu, wanda wannan zai ba ni kusan wata biyu da rabi kafin gasar Olympics, to amma ina haihuwa sai na fahimci cewa dakatar da shayarwa ba abu ne da zan iya ba. Abu ne da nake matukar so,” i n ji Tuliamuk.
Wannan na daga cikin abubuwan da suka sa hukumar wasan Olympics ta duniya da masu shirya gasar ta Birnin Paris ta shekarar nan, a karon farko a tarihin Olympic suka samar da waje na musamman na zuwa da yara gasar.
“Mun yi nazari sosai daga abubuwan da suka faru a gasar Tokyo da sauran wadanda aka yi a baya, muka yi tunanin kawo wani sauyi mu inganta gasar” kamar yadda Emma Terho, ta hukumar gasar ta Olympic ta bayyana.
Muna da tarin mata matasa da ke da jarirai kanana, da kuma mata da ke ci gaba da sana’arsu ta wasan bayan sun haihu domin a cewarta sun lura cewa za su fi mayar da hankali sosai a gasar idan akwai wuraren da za su iya ganin jariransu da masu kula da jariran a wajen gasar.
Saboda haka ne aka samar da wani waje na musamman a sansanin gasar, inda mai shayarwa za ta iya samun ganin jaririnta a kebe, ta tatsi nono a ajiye domin bai wa jaririn da dai sau-ran abubuwa na kula da jaririn.
Akwai damar ma da mai shayarwa za ta iya kwana a wajen tare da jaririnta, idan har hukumomin shirya gasar na kasashe suka yarda su samar da kudaden gudanar da su sai dai tsohuwar ‘‘yar gasar Olympic ta huturu, Terho, ta ce akwai tsarin da mai shayarwa da ke matukar bukatar wajen za ta iya nema a bata.
A cewar ta, “Muna son mu tabbatar da cewa akwai wajen da masu shayarwa da ke gasar za su iya kasancewa cikin sirri, kuma su mayar da hankali a kan gasar, to amma ina ga wuraren da ake gasar ta Olympic?
Tuliamuk ta ce wurin gasar tseren Sapporo a 2021 ba a tsara shi yadda mata masu shayarwa da ke gasar za su iya kasancewa da jariransu ba amma bayan da aka samu sauyi saboda zafi, ba ta samu damar sha-yarwa a otal din da jaririyarta da mai kula da ita da kuma mijinta suke ba.
“Na je inda za mu yi tseren inda muke da tanti na tawagar ‘yan wasan Amurka, to amma ba wajen da za ka shayar da jariri ko inda za ka tatsi nono amma da zan so na je bandaki na tatsi nonon, to amma lokaci ya kure sai dai da zai yi kyau a ce akwai wani waje na sirri , to amma ba wanda ya yi tunanin cewa za a samu mata masu shayarwa da ke gasar, ” in ji ta.
Bukatar neman canji
Terho ta ce hadin kai da aka samu tsakanin hukumar Olympic ta duniya da takwararta ta gasar Paris, shi ya taimaka wajen tabbatar da wannan sauyi, inda gwarzuwar tseren mita 200 ta gasar Olympic, Allyson Felid ta Amurka, wadda a yanzu ta yi ritaya, take kan gaba wajen tabbatar da wadannan sauye-sauye.
Ita ma tauraruwar kokawar judo Clarisse Agbegnenou, wadda ta ci lambar zinariya biyu ta Olympic, ita ma ta nemi a samar da dama ga mata masu shayarwa, a garinta kasancewar ta shayar da jaririyarta, Athena, ita ma.
Amma ba matan ba ne kadai ke wannan fafutuka ta neman canji, tsohuwar ‘yar tseren Amurka, Alysia Montano na daga cikin masu wannan gwagwarmaya, kasancewar ta taba shiga gasar kasa a 2014 a Sac-ramento, lokacin tana da cikin wata takwas.
Montano ta bayyana irin nasarorin da ta samu tare da tawagar Amurka yayin da take da jaririya, da ku-ma iin matsaloli da kalubalen da ta fuskanta a wannan yanayi kuma sakamakon irin kalubalen da ta fus-kanta da kuma na matan da take goya wa baya a wannan fafutuka, Montano, ta ce sauyin da aka samu a gasar Paris 2024, wani ci gaba ne.
Daya daga cikin manyan kalubalen mata masu shayarwa, da ke son amfani da wurin da aka samar na musamman da za su iya zuwa su kwana da jariransu shi ne yadda za su shawa kan hukumomin kasarsu su samar da kudin tafiyar da wurin.
Terho, ta hukumar shirya wasannin Olympic ta duniya, ta ce hukumar na nazarin yuwuwar samar da hakan a wasannin Olympic nan gaba, amma da farko sai an ga irin yadda tsarin ya kasance a gasar ta Par-is.
To amma ga masu fafutuka irin su Montano, akwai bukatar kara azama kafin gasar Olympic ta gaba ta Los Angeles 2028 domin Montano ta ce, za ta so ta ga an samar da wurare na sirri da suka dace a filayen wasanni, inda mata masu shayarwa za su iya zama cikin tsanaki su tatsi nononsu su ajiye domin amfanin jariransu.
Haka kuma tana son ganin an samar da damar da mata masu shayarwa za su iya kasancewa da masu kula da jariransu tsawon lokacin da suke gasar. Tuliamuk, wadda ba ta samu damar shiga gasar Paris 2024 ba saboda rauni, wadda kuma take fatan zuwa gasa ta gaba ta Birnin Los Angeles, LA 2028, tana fatan ganin ta samu tallafin da take bukata, idan ya kasance ta sake haihuwa a lokacin.
Ta ce kasancewar mace mai shayarwa tare da jaririnta, ba abin da yake sauyawa, hasali ma mace na kasancewa cike da kwarin gwiwa a gasa ta ce sun ga abin da iyaye mata za su iya yi idan aka ba su goyon baya dari bisa dari. Ya kamata su ci gaba da wannan fafutuka.