Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga sukar da Gwamna Bala Mohammed ya yi kan manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.
A lokacin kamfen É—in jam’iyyar PDP don zaÉ“en Æ™ananan hukumomi a jihar Bauchi, Gwamna Mohammed ya nuna damuwarsa game da tattalin arzikin Æ™asa, yana zargin Gwamnatin tarayya da aiwatar da manufofin da suka haifar da Æ™aruwar talauci, da yunwa, da matsin tattalin arziÆ™i a faÉ—in Nijeriya.
- Ba Wanda Zai Yi Zanga-zanga A Bauchi – Muhammad Ibrahim
- Gwamna Bala Ne Ya Jefa Al’ummar Bauchi Cikin Matsin Rayuwa Ba Tinubu Ba – Sanata Shehu Buba
A wata sanarwa da ya fitar, kakakin majalisar Suleiman ya jaddada waɗannan ra’ayoyi, inda ya bayyana cewa tasirin waɗannan manufofin na yin illa ba kawai a jihar Bauchi ba, har ma a duk faɗin ƙasa.
Ya bayyana cewa sukar da gwamnan ya yi ya yi ne duba da halin Æ™unci da ake ciki, kuma ya yi kira ga shugabanni da su tsaya tsayin daka don tabbatar da aiwatar da manufofin da ke fifita jin daÉ—in jama’a.
Suleiman ya yi kira da a sake duba manufofin Gwamnatin tarayya don tabbatar da cewa manufofin da ake aiwatarwa masu É—orewa ne kuma suna amfanar da mafi yawan jama’a.
Kakakin Majalisar ya kuma yi kira ga sauran shugabanni da su haÉ—a kai wajen kira da a sake nazarin waÉ—annan manufofin, yana mai jaddada cewa jin daÉ—in al’umma ne ya kamata ya zama ginshiÆ™in kowace gwamnati.