Tawagar kasar Sin a gasar Olympics ta Paris 2024 ta cimma burin da aka sanya a gaba na rashin samun aukuwar batutuwan da suka shafi shan kwayoyin kara kuzari, saboda da gwamnatin kasar Sin ba ta amince da shan kwayoyin kara kuzari yayin wasannin motsa jiki ba.
Mataimakin shugaban tawagar Liu Guoyong ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai jiya Lahadi, inda ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 10 ga watan Agusta, ‘yan wasa 151 da suka fafata a wasanni 35 daga tawagar wasannin motsa jiki ta kasar Sin sun yi gwajin maganin kara kuzari guda 214, wanda ya ragu daga gwaje-gwaje 230 da aka gudanar a lokacin wasannin Olympics na Tokyo. Hakan ya nuna yadda hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta kasa da kasa ta amince da tsaftar ‘yan wasan kasar Sin, da kuma ingancin matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da shan kwayoyin kara kuzari yayin wasannin motsa jiki.
Liu ya jaddada cikakken kokarin kasar Sin wajen samar da “tsaftatacciyar tawagar kasar Sin mara amfani da kwayoyin kara kuzari,” yana mai cewa, ta hanyar mai da hankali kan tsafta a bangarori daban-daban kamar tawagogin kasa da kasa, da wuraren ba da horo, da tawagogin ba da taimako, da abinci, da magunguna da abinci mai gina jiki, da ba da tallafi daga waje, da muhallin zamantakewa, da tsare-tsaren gasar da ka’idojin da’a, da wayar da kan ‘yan wasa na kasar Sin, duk an inganta su don hana damar shan kwayoyin kara kuzari. (Yahaya)