Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa mummunar akidar sayan kuri’u na kara dagula dimokuradiyyar Nijeriya.
Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron lacca da ta gudana a dakin karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta cikin Jihar Ogun.
Ya kara da cewa sayan kuri’u ya saba wa dimokuradiyya da dokokin zaben kasar nan, sannan yana da babban hukuci ake yi wa duk wanda aka kama da sayan kuri’un zabe.
Sanusi ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ake buga jabun takardun zabe da ke zama shaida kan an zabi ‘yan siyasa.
Ya ce, “Kamar yadda ‘yan Nijeriya suke kiran ‘yan siyasa su dunga bin doka, muna bukatar yin kira ga ‘yan Nijeriya da su kiyaye hakkokin da ya rataya a wuyansu kafin a samu adalci a tsakanin al’umma.
“Daya daga cikin manyan hanyoyin da suke dagule zabe shi ne, mummnuar akidar sayan kuri’u, sannan wannan mummunar dabi’a ce ta karya dokokin zabe a cikin kasar nan.
“Dole ne ‘yan Nijeriya su hada kansu wajen tabbatar da cewa an toshe duk wata hanya da ke ruguza zabe a kasar nan. Akwai bukatar mu tabbatar da cewa wadanda aka zabe ne suka hau karagar mulki a mukamai daban-daban,” in ji shi.