Tawagar Super Falcons ta Nijeriya ta ci gaba da zama ta 36 a jadawalin iya taka leda da hukumar kwallon kafa ta FIFA take fitarwa.
An fitar da sabon jadawalin a shafin yanar gizon hukumar Æ™wallon Æ™afa ta duniya yau Juma’a, 16 ga watan Agusta, 2024.
- CMG Da Kwamitin Wasanni Da Olypimcs Na Faransa Za Su Zurfafa Hadin Gwiwa
- Yanzu Ne Lokacin Da Ya Dace Arsenal Ta Lashe Kofin Firimiya – Kroenke
A Afirka, Falcons har yanzu suna matsayi na daya kuma Banyana Banyana na Afirka ta Kudu na biye da su,matsayin Falcons bai zo da mamaki ba duba da yadda aka fitar dasu a gasar Olympics ta bazara a birnin Paris.
Tawagar ta kare a mataki na karshe a rukunin da ke da Brazil,Japan da kuma zakarun duniya Spain.
Zakaran gasar Olympics na Paris, Amurka ta dawo matsayi na daya, wadda ta lashe lambar azurfa ita ma Brazil ta koma matsayi na takwas yayin da Spain ta koma matsayi na uku.
Za a fitar da jadawalin duniya na FIFA na gaba a ranar 20 ga Disamba, 2024.