Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya nanata kira ga kungiyar Houthis da ta girmama hakkin zirga-zirgar jiragen kasuwanci a tekun Maliya, kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanada.
Geng Shuang ya bayyana haka ne yayin zaman da Kwamitin Sulhu na MDD ya yi game da kasar Yemen, inda ya ce Sin na maraba da yarjejeniyar da aka cimma a baya bayan nan, tsakanin gwamnatin Yemen da kungiyar Houthis game da harkokin kudi da na zirga-zirgar jiragen sama.
- Sin Ta Harba Gungun Taurarin Dan Adam Na Binciken Doron Kasa
- Kasar Sin Ta Kafa Cikakken Tsarin Samar Da Sabbin Makamashi Mafi Girma A Duniya
Ya ce yanayin da ake ciki a Yemen da Tekun Maliya na da alaka da rikicin Gaza, ya na mai gargadin tafiyar hawainiya wajen cimma dakatar da bude wuta a Gaza, ka iya kai wa ga yaduwar tasirin rikicin da ka iya haifar da tashin hankali a yankin.
Jami’in na Sin ya kara da kira da a aiwatar da kudrorin MDD masu lamba 2712 da 2720 da 2728 da kuma 2735 nan take, domin cimma dakatar da bude wuta mai dorewa a Gaza, da kuma rage zaman dar-dar a yankin, ciki har da Yemen da tekun Maliya. (Fa’iza Mustpha)