A wasu hare-hare da dakarun sojin Nijeriya suka kai wa ‘yan ta’adda sun yi nasarar hallaka biyar tare da karbar wasu ‘yan ta’adda da iyalai 44 da suka mika wuya a jihar Borno.
Sojojin sun kuma kama wani kasurgumin barawon shanu da ake nema ruwa a jallo a Jihar Filato da kuma wani da ake zargin mai sayar da makamai ne a jihar Oyo.
- Tsadar Rayuwa A Nijeriya Ta Karu Da Kashi 19 A Wata 1
- Jihohi Sun Kashe Naira Biliyan 139.92 Wajen Biyan Bashin Kasashen Ketare A Wata 6
Sakamakon wadannan hare-hare, sojojin sun kuma kwato bama-bamai, makamai, alburusai, da shanun da aka sace.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa, a ranar 12 ga watan Agustan shekarar 2024 ne sojojin suka kai wani samame a wani sansani na ‘yan ta’addan ISWAP a karamar hukumar Bama ta jihar Borno inda suka kashe ‘yan ta’adda biyar. Sun kuma kwato Bama-bamai guda biyu, bindigogin toka guda biyu, abin durin Bomb na RPG daya, Kwanson alburushi na bindigar AK-47 Rifle daya, harsashi 23 samfurin 7.62 d 54mm, babura shida da magunguna iri-iri.
A ci gaba da farmakin da ake kai wa kungiyoyin ‘yan ta’adda a fagen yaki na Arewa-maso-Gabas, “’yan ta’addan Boko Haram 44 da iyalansu sun kuma mika wuya ga sojojin da aka tura a kananan hukumomin Bama, Dikwa da Gwoza na Jihar Borno”.
A halin da ake ciki kuma, sojoji a Jihar Filato sun kama wani da ake zargi da satar shanu, Malam Maawuya Shuaibu, a Mararaban Kantom da ke karamar hukumar Barikin Ladi a jihar.
An kama wanda ake zargin wanda ya kasance cikin jerin sunayen mutanen da jami’an tsaro ke nema bisa alaka da aikata miyagun laifuka a kananan hukumomin Barikin Ladi, Riyom da Mangu na jihar, yayin da sojojin suka dauki mataki bayan samun sahihan bayanan sirri a kan wanda ake zargin. Dakarun sun kwato shanu 32 daga hannun wanda ake zargin.
Bugu da kari, a Jihar Bayelsa, sojoji sun kai samame a maboyar miyagu da ake zargin ‘yan fashi ne a yankin Korokorosie da ke karamar hukumar kudancin Ijaw, inda suka kama wani mai suna Donald Emason tare da kwato bindigar Ribarbar guda daya da wasu bindigogi kirar gida guda biyu da wanda ake zargin ya boye.
Hakazalika, sojojin da aka tura karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo, sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne Mohammed Bello, mai shekaru 33.
Sanarwar ta kuma ce wanda ake zargin, wanda aka cafko shi daga maboyarsa, “ya amsa cewa yana daya daga cikin masu aika makamai da alburusai ga gungun masu garkuwa da mutane na Bello Chikidawoje da ke aikata miyagun ayyukansu a yankin baki daya”.