Wasu alkaluma da aka fitar, sun nuna cewar adadin wadanda da suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan da ta mamaye sassan Jihar Jigawa, ya karu zuwa akalla mutane 30.
Rahoton ya kara da cewar, baya ga wadanda aka rasa, akalla mutane dubu 9,366 ambaliyar ta raba da muhallansu, bayan mamaye gidajen da yawansu ya kai 4,699, sai kuma gonaki sama da 1000 da suka lalace.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Asibitin Ƙauran Namoda Da Ya Inganta
- Badakalar Kudade: Kotun Daukaka Kara Ta Nemi Tsohon Gwamnan Kogi Ya Gurfanar Da Kansa A Kotu
Yayin da yake karin haske kan halin da ake ciki, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar, Dakta Haruna Mairiga, ya ce gwamnati a matakin jihar ta fara tallafa wa wadanda iftila’in ya shafa ta hanyar raba musu kayan abinci da magunguna a wuraren da suke samun mafaka.
Bayanai sun ce a halin yanzu ambaliyar da ta afkawa sassan Jihar Jigawa, ta yi wa garuruwa 90 barna.
Kafin fara daminar bana Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET), ta yi hasashen cewa za a fuskanci saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a kananan hukumomi 18 daga cikin 27 da ke fadin Jihar Jigawa.
Iftila’in ambaliyar ruwa ba sabon abu ba ne a Jihar Jigawa, sai dai a ‘yan shekarun baya-bayan nan, lamarin ya yi munin da ke janyo hasarar rayuka, muhallai da kuma tarin gonakin da ake dogaro da su wajen samar da abinci.