Honarabul Aminu Boza ya ya mayar da martani kan zarginsa da hannu a kisan Sarkin Gobir, Boza ya bayyana cewar ko kaɗan babu kamshin gaskiya a zancen illa sharri, da ƙage da ƙoƙarin ɓata masa suna kan yadda yake yaƙi da ƴan bindigar daji.
Boza wanda ya bayyana hakan a tattaunawarsa da VOA Hausa ya bayyana cewar ko kaɗan bai yi mamaki ba domin duk wanda ke yaƙi da ta’addanci, ta’addanci zai yaƙe shi.
- Ɗan Sarkin Gobir Da Aka Ceto Ya Bayyana Ɗan Siyasar Da Ke Da Hannu Kan Kama Shi
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Ya ce a lokuta da dama ƴan bindigar sun yi ta neman rayuwarsa, sun yi ta aika masa saƙon kisa saboda yadda yake yaƙar su a kafafen yaɗa labarai tare da ƙin yadda da sulhu da su.
Ya ƙara da cewa, an san inda Turji yake a Fakai kusa da Shinkafi da inda Halilu Sububu yake wanda ya yi garkuwa da Sarkin Gobir don haka babu buƙatar sulhu da su illa a yaƙe su.
Dan majalisar na APC ya bayyana cewar abokan adawarsa ne a siyasa ke ƙoƙarin ɓata shi a abin da hankali ba zai taba ɗauka ba a ce ya ba da miliyan biyar domin su yi garkuwa da Sarkin Gobir.
Ya ce hatta maƙiyansa sun san irin gwagwarmaya da fadi tashin da yake yi wajen yaƙi da ta’addanci a ƙoƙarin ganin an samu zaman lafiya a ƙasar Gobir a inda ya ce kusan kashi 92 na arzikinsu ya ƙare a ta’addanci tare da hasarar gonaki masu yawan gaske.