A ci gaba da nasara da ake yi kan mayakan Boko Haram a kasashen Nijeriya, Chadi, Kamaru, da Nijar, an sake samun wasu daga cikin ‘yan bindigar da su ka mika wuya a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar.
‘Yan Boko Haram na ci gaba da tuba a Jihar Diffa da ke gabashin Jamhuriyar Nijar da ma sauran wuraren na gabashi, inda a yanzu haka mahukunta ke cigaba da karbar tubabbun mayakan Boko Haram din wadanda suka mika wuya bisa radin kansu, a wani mataki na sake saka su a cikin al’umma amma bayan horas da su ta hanyar sauya musu tunani zuwa mai kyau.
- Babban Kwamandan Boko Haram Da Wasu Mutane 9 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
- NIREC Ta Buƙaci Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro A Nijeriya
Yanzu an sake samun ‘yan Boko Haram sama da 700 da su ka tuba. Wadannan tubabbun dai a halin yanzu na gudanar mu’amalar zamantakewarsu tsakaninsu da al’umma, inda sannu a hankali su ke sabawa da rayuwar yau da kullum baya ga horas da su din da za a yin a musamman.
Jihar ta Diffa, wacce ke makotaka da Nijeriya, Chadi, ta yi fama da hare-haren Boko Haram a shekarun da su ka gabata, al’amarin da ya yi sanadin mace- macen mutane da dama ciki har da yara kanana da mata.
Wannan ya sa da dama daga cikin ‘yan yankin sun gudu zuwa wasu sassan kasar, baya ga wadanda su ka ketara zuwa wasu kasashe makobta.
Idan za a iya tunawa dai, a jihar ta Diffa tun a shekara ta 2015 aka fara rikicin Boko Haram, lokacin da har ta kai ga hukumomin yankin na ta kokarin yin yarjejeniyoyin sulhu da ‘yan Boko Haram. Bayan da aka fara cimma jituwa, sai ‘yan bindigar Boko Haram din suka fara mika wuya a 2016, inda nan take aka shiga tura su a wata cibiyar da ke sake daidaita hankalinsu jihar ta Diffa.
A shekara ta 2019 kuwa mahukuntan Jihar Diffa na lokacin suka umurci fara tura tubabbun zuwa ga ‘yan uwansu.
Malam Kyari Ari, daya daga cikin tubabbun farko da suka aje makamansu a Jihar Diffa, kuma kawo yanzu suke zaman lafiya da jama’a, ya bayyana cewa an yaudare su ne suka shiga Bako Haram. Ya yi kira ga hukumomi da su taimaka musu da abin yin sana’a don samun abin zaman gari.
Su ma mutanen gari sun bayar da kyakkyawar shaida kan tubabban ‘yan Boko Haram din da cewa suna cikakken zaman lafiya da su.