A ƙalla ƴan bindiga 37 ne aka kashe a ƙauyen Matusgi dake ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara, bayan mazauna yankin sun kai farmaki kan wata tawagar ƴan bindiga da suka mamaye ƙauyen da nufin sace mazauna yankin.
Wani mazaunin yankin ya ce ƴan bindigar, waɗanda suka iso ƙauyen a kan babura da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar Laraba, sun fara harbe-harbe don tsoratar da mutanen ƙauyen. Sai dai, mutanen yankin da suka yi shiri da bindigogin gargajiya da makamai na al’ada sun fuskanci maharan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
- An Kammala Gasar Tseren Dawakai Ta Ƙasa-da-ƙasa A Jihar Kano
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Fafatawar ta ɗauki tsawon sa’a guda, inda mutanen ƙauyen suka samu nasarar kashe ƴan bindiga 10, hakan ya tilasta suka janye. Daga nan ne mutanen yankin suka sake haɗuwa suka yi kwanton ɓauna, wanda ya haifar da sake kashe ƙarin ƴan bindiga 27 yayin da suka dawo.
Hakimin Matusgi, Alhaji Ciroma Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kuma bayyana cewa mutane uku daga cikin mazauna yankin sun rasa rayukansu yayin artabun.
Alhaji Muhammad ya kuma nuna damuwa cewa wannan hari shi ne karo na 13 da ƴan bindiga suka kai wa ƙauyen. Ya yi karin bayani kan wani harin da ya faru makonni uku da suka gabata, inda aka yi garkuwa da mutane 23, galibinsu mata, kuma aka buƙaci fansar Naira 150,000 a kan kowane mutum.
Duk da biyan kuɗin, an sako mata bakwai kaɗai, yayin da ragowar ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da su.