A halin yanzu gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, jami’o’i 8 en kawai ta amince da takardun shaidar digirisu, sune kuma ta amince ‘yan Nijeriya su je su yi karatu a cikinsu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke aikin tantance takardar digirin bogi a fadi tarayyar kasa nan.
- BUK Ta Karrama Farfesa Rasheed Bayan Ya Shafe Shekaru 7 A Hukumar NUC Ta Kasa
- Jerin Jami’o’i 18 Da NUC Ta Haramta Karatu Acikinsu
Sanarwar haka ya fito ne daga bakin Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, a tataunawar da ya yi da gidan talabijin na Channels.
Farfesa Mamman yana magana ne a daidai bikinn cikarsa shekara daya a kan karagar mulki, ya kuma ce, fiye da ‘yan Nijeriya 22,500 ke dauke da takardar digiri a bogi daga kasashen biyu, ya jaddada cewa lallai za su soke amfani da takardun shaidar a tare da bata lokaci ba.
Ya ce, wannan na daga cikin bangaren rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa domin duba yadda ake cuwa-cuwar samu takardar digiri daga jami’o’in kasashen waje da na cikin gida.
Ministan ya kara da cewa, lamarin binciken ya taso ne bayan da wani dan jaridar Nijeriya ya binciken kwakwafi har ya samu takardar digiri daga jami’ar kasar Benin a cikin wata 2 kuma har ya samu shiga tsarin yi a kasa hidima NYSC.
A kan haka ministan ya ce, gwamnatin tarayya ta amince ne kwai da jami’a 3 daga kasar Togo da 5 daga kasar Benin, yayin da ta ayyana sauran a matsayin haramtattu.
Ya ce, jami’o’in da aka amince da su a kasar Togo sun hada da ‘Unibersite De Lome’, ‘Unibersite De’ Kara da ‘Catholic Unibersity of West Africa’.
Haka kuma jami’o’i biyar da aka amince da su a kasa Benin sun hada da ‘Unibersite D’abomey-Calabi, Unibersite De Parakou, Unibersite Nationale Des Sciences, Technologis Ingenierie Et Mathematikues; Unibersite Nationale D’ Agriculture da Unibersite Africaine De Deblopment Cooperatif.
Ministan ya kuma jaddada cewa, babu gudu babu ja da baya a kan shawara gwammatin tarayya na soke takardar digiri 22,700 da wasu ‘yan Nijeriya ke dauke da su daga wadannan jami’o’in kasashen waje.
Ya kuma ce, wannan hukuncin da aka yanke ya yi daidai domin masu dauke da irin wannan takardar digiri suna bata sunan Nijeriya ne da kuma karya darajar matsayin ilimi a cikin gida Nijeriya.
Ya ce, da ya a daga cikin masu dauke da wannan takardrar digirin basu ma fita kasar ba amma an samar musu da dirigin ta hanyar cuwa-cuwa tare da hadin kan wasu jami’an gwamnatin kasashen waje dana cikin gida.