Wata kididdiga da kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin ya fitar ta nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2023, kasar Sin ta aike da masu aikin jinya har dubu 25 zuwa kasashen Afirka daban daban, wadanda suka ba da jinya ga mutane miliyan 230.
Kasar Sin ta fara tura tawagogin likitoci zuwa kasashen Afirka tun daga shekarar 1963. A halin yanzu, akwai tawagogin likitocin kasar Sin 44, kunshe da mutane 863, wadanda suke aiki a cibiyoyin ba da jinya 94 a kasashen Afirka 43.
A halin yanzu, kasar Sin ta riga ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da asibitoci 46 dake kasashen Afirka 41, inda aka kafa cibiyoyin hadin gwiwa 25, wadanda suka shafi fannonin jinyar ciwon zuciya, da na koyar da ilimin likitanci na kula da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali da dai sauransu, yayin da aka samar da fasahohi masu dimbin yawa ga kasashen da abin ya shafa. (Mai Fassara: Maryam Yang)