Dangane da abin da ya shafi karin kudin mai da gwamnati ta yi, mun lura da irin cin amanar da gwamnatin tarayya ta yi asirce na kara wannan farashi. Kuma a fahimtarmu shi ne daga daga cikin dalilan amincewa da Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi, wanda mun sani cewa gwamnati ba za a kara farashin duk da cewa Naira 70,000 din ma ba za ta wadatar da ma’aikata ba.
Mun tuna a fili lokacin da shugaban kasa ya bamu zabe cewa: ko dai Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma za a yi karin kudin mai tsakanin Naira 1,500 zuwa Naiar 2,000) da kuma Naira 70,000 (a tsohon farashi)., sai muka zabi na karshe. Mun yi haka ne don ba za mu yi sanadin jefa ’yan Nijeriya a kuncin rayuwa ba.
- A Gaggauta Janye Ƙara Farashin Man Fetur – NLC Ga Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Sayar Da Buhun Shinkafa Kan Dubu 30
Sai gashi wata daya da ayyana hakan amma gwamnati ba ta fara biyan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ba kuma ta zo da wani sabon lamari da za mu lamunce shi ba.
Gaba daya lamarin ya zama wani mafarki mai ban tsoro
Amma duk da haka, lokacin da muka gaya wa gwamnati cewa matakin da za a bi don magance wannan lamari ba zai haifar da da mai ido ba, kuma ba abu ne da zai dore ba, sai wasu shugabanni daga cikinsu suka rika yi mana izgilanci cewa, ba mu fahimci asaln yadda tattalin arziki yake ba.
To amma idan za a kalli gaskiya, wannan aikin ne na cin amana da ya yi daidai da halayyar wannan gwamnati. Mun tuna da tabbacin da shugabannin majalisar suka ba mu kan karin kudin fito na kashi 250% na cewa an magance shi kuma babu bukatar sai an gabatar da Ministan wutar lantarki da ke wajen taron.
Maimakon a dawo da batun tsohon farshin da aka yi alkawari tun daga wancan lokacin, ai kawai sai farashin man ya sake tashin gwauron zabo inda ya kara jefa ‘yan Nijeriya da ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Maimakon yin gyara, gwamnati ta kama tare da tsare wasu daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar, wasu kuma wadanda ba su da alaka da wannan zanga-zangar, tana tuhumar su da laifin hada baki, zagon kasa, cin amanar kasa, bayar da kudaden ta’addanci da kuma aikata laifuka ta intanet da nufin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu.
Tuni dai ‘yansanda da sauran jami’an tsaro suka ci gaba da addabar al’ummar kasar domin cimma manufofin gwamnati na murkushe ‘yan adawa masu mutunci.
Suka yi tsayin daka wajen bata suna da kuma tozarta dimbim al’umma.
Sun yi nisa wajen daidaita ayyukan da doka ta tanada na Ma’aikatar Kwadago da Aiki wajen warware batutuwan da suka shafi kasuwanci da kuma batutuwan da ba su dace da hukumomin tsaro ba.
A halin da ake ciki gwamnati na ta muzgunawa gami da takurawa rayuwar al’umma, wanda kuma hakan ba karamin al’amari bane, amma muna yi wa ‘yan Nijeriya alkawari cewa mu a Kungiyar Kwadago ta Nijeriya, tare da kungiyoyin farar hula ba za a yi wa kasa biyayya ba, kuma mu muka kawo wannan dimokuradiyya a lokacin da wasu daga cikin masu rike da madafun iko a yau suke hada baki da sojoji kan yadda za su ci gaba da rike madafun iko na siyasa.
Lokacin da Jami’an tsaro suka kama mu a wannan gwagwarmaya, mun sha zargi. Mun san sun suna da wani mugun nufi da kuma bukatar su karkatar da hankalinmu ko su firgita mu ko raunanawa mu don kada mu sami amsa mai kyakkyawar hujja.
Yanzu dai burinsu ya cika, kuma gaskiyarmu ta bayyana a cikin zargin da muka yi musu. Duk da haka, muna so mu sanar da ‘yan Nijeriya cewa sun cimma burinsu na kara farashin man fertur wanda shi ne na farko a cikin daidaitattun manufofin da gwamnati ke kai.
A namu bangaren, mun tsaya tsayin daka kan hakkin jama’a, kuma ba za mu bari gwamnati ko jami’anta na tsaro su janye hankalinmu ba ko kuma su tsorata mu.
Saboda haka, muna bukatar aiwatar da wadannan abubuwa cikin gaggawa::
1). Janye sabon farashin man fetur da aka kara;
2). Sakin duk wadanda ake tsare da su ko kuma ake tuhumar su bisa zaton sun shiga zanga-zangar kwanan nan;
3). Dakatar da kamawa gami da tsare ’yan kasa bisa zargin karya;
4). Janye karin kudin wutar lantarki;
5). Kawo karshen yin sama da fadi da ayyukan Ma’aikatar Kwadago da Aiki;
6). Kawo karshen manufofin da ke haifar da yunwa da rashin tsaro;
7). Dakatar da dabi’ar gwamnati na ta’addanci, tsoro da karya.
‘Yan Nijeriya Na Cikin Tsaka-mai-wuya Yayin Ake Sayar Da Litar Mai Naira 1,000
‘Yan Nijeriya a sassan kasar sun shiga halin damuwa da tsananin kokawa yayin da tilas ta sanya suke sayan litar man fetur a kan kudi har naira 1,000 a sassa daban-daban da suke fadin kasar.
Wannan lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da matatar man Dangote ta bai wa kamfanin kula da albarkatun mai ta Nijeriya (NNPCL) damar ficewa daga tsarin shigo da mai daga kasar waje domin za a iya share mata hawayenta a cikin nan gida Nijeriya muddin ta amince.
Tun da farko dai, matatar man Dagote da ke Legas ta tabbatar wa majiyarmu cewa tana da karfin fitar da ganga 650,000 kowace rana.
A cewar jami’in watsa labarai na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya ce, man Dangote tabbas zai iya share wa al’ummar Nijeriya hawaye da dogon layin neman mai da suke kan yi gami da wahalar samun mai din.
“Kamfanin ya fara sarrafa man fetur. A daidai lokacin da ya kai matakin shiga kasuwa za ku ga tasirinsa.
Fara sarrafa man Dangote na zuwa ne daidai lokacin da kamfanin NNPCL ke fargabar yadda ake kashe maguden kudade wajen biyan kudin jigilar mai da kuma tulin basukan da ake bin dillalai mai da ya haura sama da dala biliyan 6.
Kakakin kamfanin, Olufemi Soneye, ya shaida cewar kalubalen yawan kudade na barazana ga daurewar jigilar mai a kasar nan. Babban matsalar dai shi ne, kudin shigo da mai daga waje.
Bayanin bazaranar kudi na NNPCL ya ta da hankula, inda masu ruwa da tsaki a bangaren mai da iskar gas suka dukufa tofa albarkacin bakinsu.