Gwamnatin tarayya ka iya kashe a kalla naira biliyan 188.25 a kowace shekara wajen biyan tallafin kudi na wutar lantarki ga asibitocin gwamnati sama da 75 da manyan makarantu su 300 a sassan kasar nan.
Wannan na zuwa ne biyo bayan amincewa da gwamnatin tarayya ta yi da sassaucin kaso 50 cikin 100 na kudin lantarki ga asibitocin gwamnati da kuma manyan makarantu a fadin Nijeriya.
- Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Zuwa Jana’izar Mahaifiyar Yar’Adua
- Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Ƙaddamar Da Aikin Noma Ga ‘Yan Gudun Hijira A Filato
A watan Afrilu ne hukumar kula da wutar lantarki ta sanar da karin kudin wutar lantarki ga masu amfani da rukunin A na karin kudi da aka samu da kaso 300.
Tun da farko dai, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa wa asibitoci da manyan makarantun da suke mallakinta wajen rage musu kudin wutar lantarki da suke biya.
Ya ce, gwamnati tana sane da irin kudin da asibitoci da manyan makarantu ke kashe wajen biyan kudin wuta, wanda hakan ya zama musu babban kalubale.
Karamin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa, ya sanar a ranar Alhamis cewa gwamnatin tarayya ta amince da biyan tallafin lantarki na kaso 50 ga asibitocin gwamnati.
A cewar Alausa, wannan an yi ne domin rage wa asibitocin kashe maguden kudade wajen biyan kudin wuta wanda hakan ke shafar majinyata da ya sanya ake cazansu kudi da yawa.
Binciken da majiyarmu ta gudanar, ya nuna cewa gwamnatin tarayya za ta iya kashe naira miliyan 50 ga kowace asibiti daga cikin sama da 75, inda ya kai kimanin biliyan 3.75 a kowace wata, wato biliyan 45 a shekara guda.
Shugaban kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas, Dakta Ibraheem Abdul, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa wannan, yana mai cewa tabbas hakan zai taimaka wajen kyautata koyarwa da kuma rage wa makarantu tsula kudi ga dalibai.