Jami’an Hukumar Yaki Da Cin Hanci ta Kasa (EFCC) sun yi dirar wa kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Wuse Zone 4 a Abuja da zummar kamen masu boye Dalar Amurka.
Daily Trust ta ruwaito cewa, EFCC ta dauki matakin ne don zakulo ‘yan kasuwar da ke saya sannan suna boye kudaden kasar waje musamman Dalar Amurka, abin da ya sa darajar kudin kasar, Naira ke faduwa a kwanan nan.
- Ana Fargabar Yin Garkuwa Da Taurarin Nollywood A Enugu
- Kwakwanso Ya Gargadi Sanatoci Kan Barazanar Tsige Buhari
Wata majiya ta ce samamen ya biyo bayan shirin da suka dade suna yi, inda suka dinga sa ido kan ‘yan canjin da ake zargin suna sayen dalar don boyewa da kuma fita da ita daga Nijeriya.
EFCC ta tura jami’anta zuwa manyan filayen jirgin sama na kasa kamar a Kano da Legas da Fatakwal da zummar kama masu yunkurin fita da kudin, a cewar rahoton.
A ranar Alhamis ne darajar Naira ta yi mummunar faduwar da ba ta taba yi ba, inda aka dinga canzar da Dala daya a kan Naira 705 a kasuwar bayan fage.
Hakan ne ya sanya Majalisar Dattawa gayyatar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele don yi mata cikakken bayani game faduwar darajar Naira.