Ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, an samu cikakkiyar nasara a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024.Â
Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai tare da ministan harkokin wajen Senegal Yacine Fall, da ministan harkokin wajen jamhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso.
- Shugabannin Afirka: FOCAC Ya Zama Abun Misali Mai Kyau Ga Inganta Hadin-Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
- FOCAC: LEADERSHIP Da CMG Sun Sake Ƙarfafa AlaÆ™ar HaÉ—in GwiwaÂ
Da yake karin haske kan manyan sakamako da aka cimma a taron, Wang ya ce, an daukaka dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya da kasar Sin zuwa matsayin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Kana, an daga darajar dangantakar Sin da Afirka baki daya zuwa wata al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a dukkan fannoni na sabon zamani.
A nasu bangare kuwa, Falla da Gakosso cewa suka yi, hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin ya sauya makomar Afirka, kuma ko shakka babu zai shiga tarihi a matsayin abin koyi na hadin gwiwar kasa da kasa.
Game da hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da kasashen duniya, Wang Yi ya bayyana cewa, yanzu idanun kasashen duniya suna koma kan nahiyar Afirka, da kara maida hankali ga nahiyar ta Afirka. Kuma Sin na jin dadin ganin hakan a matsayinta na abokiyar nahiyar Afirka, kana tana maraba da kasa da kasa su kara nuna goyon baya da taimakawa nahiyar Afirka. Wang Yi ya bayyana cewa, akwai ka’idar musamman kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a dogon lokaci.
Na farko dai, kada a tsoma baki kan harkokin cikin gida na Afirka. Na biyu, a yi la’akari da bukatun bunkasuwa na Afirka. Na uku, kada a yi takarar siyasa tsakanin bangarori daban daban a nahiyar Afirka.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya yi bayani kan hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da kasashen duniya, inda ya ce Sin tana fatan kasa da kasa za su cimma ra’ayi daya kan wannan batu. Ya kara cewa, ya kamata a kiyaye adalci, wato Afirka tana da hakkin samun bunkasuwa, wannan ba hakkin ba kebabbe ne ga wasu kasashe. Kana a kiyaye cimma zaman daidai wa daida, wato a saurari ra’ayoyin Afirka a ko da yaushe, da girmama jama’ar Afirka wajen neman hanyoyin samun bunkasuwa da kansu. Hakazalika kuma a yi aiki domin samun moriya, wato ya kamata a yi hadin gwiwa mai amfani don kawo wa jama’ar Afirka moriya. (Mohammed Yahaya, Zainab Zhang)