Jiya Alhamis, an bude taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na 2024 wato FOCAC a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron tare da ba da jawabi, inda ya yi kira da su tabbatar da zamanintar da al’umommi a bangarori 6 cikin hadin gwiwarsu, tare da sanar da manyan ayyuka 10 cikin hadin gwiwa, matakin da ya tabbatar da alkiblar zamanintar da al’umommin Sin da Afirka cikin hadin kai.
Taswirar zamanintar da al’umommin Sin da Afirka bisa bangarori 6 da Sin ta gabatar, ta yi watsi da ka’idar nuna fin karfi, kuma ta shigo da dabarar da Sin take da ita wajen aiwatar da ayyukan zamanintar da al’ummarta, kuma ta bayyana ra’ayi mai dacewa da zamani mai daidaici a duk fannoni, wanda kuma ya dace da bukatun raya Sin da Afirka.
- An Zartas Da Hadaddiyar Sanarwa Game Da Zurfafa Hadin Gwiwa A Tsakanin Sin Da Afirka Bisa Tsarin Shawarar Ci Gaban Duniya A Taron Koli Na FOCAC
- Shugabannin Afirka: FOCAC Ya Zama Abun Misali Mai Kyau Ga Inganta Hadin-Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
Manyan ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka guda 10 sun yi la’akari da bukatun kasashen Afirka cikin gaggawa, kuma sun dace da halin da ake ciki da ma amfani da fifikon Sin da Afirka.
Wadannan matakai na bayyana cewa, Sin na bayyana sahihancinta wajen taimakawa Afirka da ta samun bunkasuwa ta hanyar dogaro da kai, ta yadda za a amfanawa jama’ar Afirka daga hadin gwiwar Sin da Afirka. (Amina Xu)