Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa yunwa mutane 10 da ake tuhuma da yunkurin hambarar da gwamnatin shugaban Bola Tinubu, kan Naira miliyan 10 kowannensu.
Da yake yanke hukunci kan bukatar bayar da belin, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ce wajibi ne masu zanga-zangar su gabatar da mutanen da za su tsaya musu.
- Hasashen Ambaliya: Gwamna Nasir Ya Kafa Kwamitin Daukar Matakin Gaggawa A Kebbi
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi A Kano
Ya ce dole ne su kasance sun mallaki gida ko fili a Abuja kuma su mika takardun kadarorinsu ga kotu.
Har wa yau, kotun ta umarci kowanne daga cikin wadanda ake tuhumar ya samar da mutum guda mazaunin Abuja da zai tsaya masa tare da mika fasfon tafiye-tafiyensa da kananan hotunansa guda uku.
Yayin da yake fatali da korafin babban sufeton ‘yansanda kan bukatar bayar da belin wadanda ake tuhumar, Mai Shari’a Nwite ya kuma umarci su da kada su sake shiga wani gangamin jama’a tsawon lokacin da suke fuskantar shari’a.
Haka kuma alkalin ya bayar da umarnin ci gaba da tsare mutanen a gidan kaso har sai sun kammala cika sharudan bada belinsu.
Idan ba a manta ba an gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a fadin Nijeriya daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Sai dai zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu sassan Nijeriya.