Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya kafa kwamiti mai mambobi 16 domin daukar matakin gaggawa don rage radadin ambaliyar ruwa da ake sa ran za ta shafi kananan hukumomi da dama a jihar.
Kwamitin wanda Mataimakin Gwamna, Sanata Umar Abubakar Tafida zai jagoranta, an kafa shi ne a yayin gudanar taron Majalisar zartawa na wata-wata da Gwamna Nasir ya jagoranta a gidan gwamnatin da ke Birnin Kebbi.
- Me Ya Sa ’Yan Kasuwar Waje Ke Sha’awar Zuba Jari A Kasar Sin
- Babu Bukatar Tada Hankali Kan Karuwar Farashin Mai – IPMAN Ga ‘Yan Nijeriya
Kwamishinan yada labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmadu ne ya bayyana wa manema labarai jim kadan bayan kammala zaman, inda ya bayyana cewa, gwamnan ya ba da umarnin daukar matakin gaggawa domin kaucewa mummunan sakamako kan yawan ambaliyar ruwa da ake samu.
Haka kuma, ya bayyana cewa, kwamitin zai zakulo hanyoyin da za a bi wajen samun sauki da mafita ga ambaliyar ruwa da ake samu don sauwaka wa al’ummomin da abin ya shafa, tare da yin hulda da shugabannin addini da na al’umma domin baiwa gwamnati damar rage wahalhalu da kuma iya kwashe al’ummomin da ke cikin hadari zuwa tudu.
Kwamitin ya kunshi kwamishinoni daga ma’aikatu daban-daban da suka hada da kwamishinan yada labarai da al’adu da kwamishinan ayyukan jin kai da wayar da kan jama’a da kwashinan albarkatun ruwa da dai sauransu da kuma shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kebbi wato SEMA, Muhammad Bello Yakubu. Yayin da Sakataren zartarwa na SEMA, Abubakar Abdullahi zai kasance sakataren kwamitin.
Gwamnati na da burin tabbatar da tsaro a dukkan al’ummomi kuma tana daukar matakan da suka dace don rage illar ambaliyar da ke tafe.