Bayan ƙorafi da kiraye-kiraye na sassauta farashin kuɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano, shugaban hukumar zaben ta jiha Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya sanar da rage kuɗin tsayawa takarar shugaban ƙaramar kukuma da kansila a yau.
Farfesa Malumfashi ya shaida hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki dangane da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe a wata mai kanawa.
- Jihar Kano Ce Za Ta Fara Aiwatar Da Sabon Mafi Karancin Albashi – Gwamna Yusuf
- Shirin X Space Na LEADERSHIP: Tabbas Gwamnatin Kano Ta Hau Turbar Bunkasa Ilimi – Mahalarta
Ya ce rage kuɗin takardar tsayawa takarar ya biyo bayan umarnin kotu bayan da wasu jam’iyyun adawa suka shigar da hukumar ƙara dangane da yawan kuɗin na takardar tsayawa takarar.
Farfesa Sani Lawal ya ce a halin yanzu hukumar zaɓen ta jiha ta mayar da kuɗin takardar tsayawa takara a matakin shugaban ƙaramar hukuma da mataimakinsa Naira Miliyan 9, wanda Naira miliyan 10 ne a baya, yayin da kuma takardar tsayawa takara a matakin Kansila ta dawo Naira miliyan 4 saɓanin Naira Miliyan 5 a baya.
Ya ce a halin yanzu hukumar ta kammala shirye shiryen fara sayar da waɗannan takardu daga ranar Litinin mai zuwa 15 ga watan Satumba 2024.