Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya kaddamar da tashar ruwa ta kamun kifi, wadda kamfanin kasar Sin ya tallafa wajen gina ta a yankin Jamestown na bakin teku, wanda ke wajen birnin Accra, fadar mulkin kasar.
An kaddamar da tashar ruwan wadda kamfanin CRCC Harbor da Channel Engineering Bureau Group ya gina ne a ranar Juma’a, ta kuma kunshi ginin ofisoshi masu hawa biyu, da kasuwar kifi, da wurin samar da kankara, da shaguna, da wurin ajiya mai sanyi, da wurin renon yara, da ofishin kashe gobara, da sashen gyaran jiragen ruwa.
Yayin bikin kaddamarwar, shugaba Akufo-Addo ya bayyana jin dadinsa game da kammalar aikin, yana mai cewa, tashar za ta bunkasa sana’arsu, da rage asarar albarkatun ruwa da ake samarwa a yankin. Kaza lika, sabuwar tashar za ta samar da sabbin guraben ayyukan yi, da habaka tattalin arziki, da sauya yanayin rayuwar al’ummun dake wurin da aka gina ta.
A tsokacin da ya yi yayin mika tashar ga gwamnati, jakadan Sin a kasar Ghana Tong Defa, ya jaddada kudurin kasar Sin na taimakawa bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Ghana. Ya ce, aikin alama ce dake tabbatar da kudurin sassan 2 na neman zamanantarwa, kana ya tabbatar da karfin gwiwa da kasashe masu tasowa ke da shi ta fuskar dunkulewa, da gudanar da ayyuka cikin hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)