Kamfanin Man Fetur na ƙasa NNPCL ya sanar da farashin man fetur da za a samu daga Matatar Dangote a watan Satumba 2024, inda farashin zai iya haura N1,000 kowace lita a wasu yankunan ƙasar nan.
Bisa ga bayanan da aka fitar, farashin zai bambanta daga wuri zuwa wuri: a Lagos zai kasance N950 kowace lita, Sokoto N992, Oyo N960, Kano da Kaduna N999, FCT N992, Rivers N980, yayin da a Borno farashin zai kai N1,019 kowace lita, wanda shi ne mafi tsada.
NNPCL ta bayyana cewa bisa ga dokar PIA, gwamnati ba za ta ƙara daidaita farashin man fetur ba, sai dai an bar shi ne ga kasuwa ta yi alƙalanci. Haka kuma kamfanin ya tabbatar da cewa an biyan kuɗin man fetur da za a ɗiba daga Matatar Dangote a watan Satumba da kuɗin Amurka dala ($), amma daga ranar 1 ga Oktoba, 2024, za a fara amfani da Naira a duk ma’amalolin ciki.