Rundunar ƴansandan Jihar Legas ta kama wasu mata biyu, Ujunwa Una da Chinelo Igbechionwu, bisa zargin haɗa baki don sayar da jarirai tagwaye.
An kama su ne a tashar Berger a Legas a ranar 9 ga Satumba, 2024, bayan wani mutumin kirki ya bayar da bayanan sirrin da ta tona asirinsu.
- FRSC Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 16 A Wani Haɗarin Motoci A Hanyar Legas
- DSS Ta Kama Tsohon Editan BBC, Adejuwon Soyinka A Filin Jirgin Sama Na Legas
Kakakin Rundunar Ƴansandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an samu mata biyun tare da jarirai mata masu kwana shida a hanyarsu daga Jihar Abia zuwa Legas. Da ake musu tambayoyi, matan sun amsa cewa an biya su ₦150,000 don ɗaukar jariran da mahaifiyarsu ta sayar saboda rashin iko da kula da su.
An mika batun zuwa sashen kula da kakkokin mata na rundunar, kuma an kai jariran gidan marayu domin kulawa. Ana ci gaba da bincike domin kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, kuma an gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.