Wasu masu kare hakkin ‘yan Adam a Jihar Kaduna sun shigar da kara a gaban kotun Majistari da ke da zama a titin Daura Road, mai lamba 37.
Sun shigar da karar ce, don kotun ta sake bude shari’ar yaron nan Almajiri dan shekara 13 da wani mai suna Isah Abdullah daya daga cikin hadimin ‘yar majalsair dokin jihar Kaduna Munirat Suleiman mai wakilitar mazabar Saminaka ya yi wa fyade.
- Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Danyen Aikin Dake Barazanar Jefa Yankin Cikin Wani Bala’i
- Xi Ya Jaddada Ba Da Cikakkiyar Dama Ga Fa’idar Siyasa Ta CPPCC
A cewasu, ba su amince da wancan hukukuncin da alkalin kotun Majistari mai lamba 2 Mai Shari’a Aliyu Dogara ya yanke na wanke Isah Abdullah da kuma sakinsa ba.
Idan za a iya tunawa, binciken da sashin manyan laifuka na rundunar ‘yansandan a Jihar Kaduna ya yi, a kan zargin ya gabatar da Isa gaban kotun mai lamba 2, wanda kotun ta bayar da umarni a ajiye Isah a gidan gyaran hali na jihar, kafin ma’aikatar Shari’ar jihar ta bayar da shawara a kan zargin.
Amma bayan jiran shawara daga ma’aikatar Shara’a ta jihar, ta wanke Isa a sakamakon rahoton gwaji da aka samu daga Asibiti a Saminaka da kuma Asibitin koyarwa na Barau Dikko.
Sai dai, masu kare rajin hakkin ‘yan’adam a jihar, sun bayyana cewa, ba su amince da wancan hukuncin kotun da kuma takardun gwajin lafiyar yaron da Asibitin Barau Dikko da Garin Saminaka suka yi a kan Almajirin ba, inda suka sake garzayawa kotun ta Majistari da ke mai lamba 37, don ta bude Shari’ar.
A hirarsa da ‘yan jarida a Kaduna daya daga cikin masu kare rajin Marwan Yabo ya ce, wancan hukuncin da kotun Daura Road mai lamba 2 ta yanke bamu yarda da shi ba.
A cewarsa, masu kare wanda ake zargin a gaban kotun, sun yi amfani da wasu takardun da aka yiwa yaron gwaji ne, a wani Asibiti da ke a Saminaka da kuma gwajin da aka yi, a Asibitin Barau Dikko, kuma takardun gwajin da aka yi, a wadannan Asibitocin biyu, na hannun mu.
Ya ci gaba da cewa, akwai kuma wasu takardu biyu wadanda suke nuna cewa, wai daga Asibitin Saminaka da kuma na Barau Dikko ne, aka bayar.
Ya kara da cewa, “To amma bamu san yadda aka yi suka samo wadannan takardun biyu ba, domin Asibitin Barau Dikko, a baya da kansu ne suka yi wa yaron gwaji suka kuma tura shi zuwa Asibitin kashi na Dala, da ke a Kano don a yi wa yaron aiki”.
Ya ce, bayan kotun mai lamba 2 ta bayar da umarnin cewa, a ajiye Isah a gidan gyran hali na jihar har sai yaron ya samu lafiya kafin a fara shari’ar, sai kawai muka ji cewa, wai kotun mai lamba 2 ta wanke Isah daga zargin, alhali ba a ma fara shariar gadan-gadan ba, kuma ba ji ta bakin yaron a kan me ya faru ba.
Shi ma daya mai kare hakiin ‘yan’adam kuma lauyan yaron Barista Sani Shehu a zantawarsa da ‘yanjarida ya ce, za su tabbatar an binciki wancan hukuncin da kotun mai lamba 2 ta yanke, inda ya kara da cewa,”Muna zargin akwai shubuha a cikin hukuncin da kotun mai lamba 2 ta yanke”.
Ya ce, idan har ita ma’aikatar shari’a ta kamar yadda takardun suka nuna cewa, ta dogara ne da wasu takardu na likita wadanda mai yiwuwa, wadancan takardun na likitan an kawo su ne ta bayan fage, ma’aikatar kuma ta yi abin da ta yi, doka ta bamu damar muma mu sake bude wata sabuwar shari’a.
Ya ce, ita kuma kotun da ta wanke wanda ake zargin, “Muna da ikon mu nemi kotu ta sama, ta warware wancan hukuncin na kotun ta 2, don a sake wani bincike don mu gabatar da dalilanmu”.