Rahotanni daga Jihar Filato, sun tabbatar da rasuwar Aliyu Abdullahi Obobo, wanda aka fi sani da “Legend from Allah”.
Marigayin ya rasu ne a Jos, babban birnin Jihar, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
- An Gurfanar Da Tsohon Alkali A Kotu Kan Zargin Lakada Wa Matar Aure Duka
- Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Danyen Aikin Dake Barazanar Jefa Yankin Cikin Wani Bala’i
Ya yi fice wajen yin tafiye-tafiye a kan keke zuwa garuruwa da dama a Nijeriya.
Talla
Tafiyar da ya yi a baya-bayan nan, ita ce wadda ya je Jihar Kano, inda ya gana da Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II.
Ya je jihohi da dama a faɗin ƙasar nan tun daga lokacin da ya fara tafiye-tafiye a kan keke.
Sannan ya taba zuwa ƙasar Saudiyya, inda a hanya ya tsaya a kasashe irin su Sudan.
Talla